Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III, ya bayyana cewa gobe Lahadi ce za ta zama 1 ga watan Muharram na sabuwar shekarar Musulunci ta Hijira 1446.
Shugaban kwamitin da ke bai wa Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addini, Farfesa Sambo Wali Junaid ne bayyana hakan a ranar Juma’a.
- Shin tsoffin shugabanni na tasiri wajen samun mulkin Nijeriya?
- HOTUNA: ’Yan Tijjaniya sun yi taron zikiri a Fadar Nassarawa
Farfesa Junaid ya ce kwamitin haɗin gwiwa da kwamitin ganin wata na Nijeriya sun tabbatar ba a samu ganin watan Muharram na shekarar 1446 a ranar Juma’ar ba, abin da ke nuna ranar Asabar za ta zama 30 ga watan Zhul Hijja na shekarar 1445.
“Sakamakon haka, Asabar [6 ga watan Yuni] ta zama 30 ga watan Zulhijja 1445…Lahadi kuma [7 ga Yuni] ta zama 1 ga watan Muharram 1446,” a cewar shugaban kwamitin ganin wata na fadar sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali cikin wata sanarwa.
“Sarkin Musulmi na taya Musulmin Nijeriya murna [sabuwar shekara] da kuma roƙa musu alheri da taimakon Allah,” in ji sanarwar.
Sarkin Musulmin ya roƙi jama’a su ci gaba da addu’ar zaman lafiya da samun ci gaba a ƙasa baki ɗaya.
A tsarin Musulunci, kowane wata kwana 29 ne amma idan aka kasa ganin jaririn sabon wata akan cika watan zuwa kwana 30.