Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci da ke Fadar Sarkin Musulmi, ta bayyana ranar Lahadi 11 ga watan Yuli, a matsayin ranar 1 ga watan Dhul-Hijjah, 1442 a Najeriya.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar da yammacin Asabar.
- Allah Ya yi wa Sarkin Lafiagi Alhaji Sa’adu Kawu rasuwa
- Jarumin Kannywood Sani SK yana neman taimako
A ranar Juma’a ne dai mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci al’ummar Musulmin Najeriya da su fara duban watan Babbar Sallah na Zul-Hijjah daga ranar Asabar wanda ya yi daidai da 10 ga watan Yulin 2021.
Sarkin, wanda kuma shine Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya, ya ce hakan ya biyo bayan ganin watan da aka yi a wasu sassa na kasar.
Watan Zul-Hijja dai shine wata na 12 a shekarar Musulunci wanda a cikinsa ne ake gudanar da bikin Sallar Layya da ma Aikin Hajji a kasar Saudiyya.
Sai dai a bana ma kasar ta Saudiyya ta takaita adadin mutanen da za su gudanar da aikin hajjin zuwa 60,000 kacal, kuma suma dole su kasance mazauna cikin kasar saboda annobar COVID-19.