Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2023 na Naira tiriliyan 19.76 ga Majalisar Dokoki ta Tarayya a ranar Juma’a 5 ga watan Oktoba da muke ciki.
Sanarwar dai na kunshe ne cikin wata wasika da ya aika ga Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Ahmad Lawan, wacce ya karanta a zauren Majalisar ranar Talata.
- Kamfanin NNPC ya samu ribar biliyan N674 a wata 12
- Dalilin da nake neman na kaina duk da arzikin mahaifina —Yayar Davido
Wasikar dai ta bayyana cewa Buharin zai gabatar da kasafin ne da karfe 10:00 na safiya, a zauren Majalisar Wakilai ta wucen gadi.
Shugaban Majalisar Dattijan ya ce tuni aka kammala shirye-shiryen karbar dukkan ’yan Majalisun da kuma ’yan rakiyar shugaban kasa.
Kamar dai yadda aka sani, yanzu haka ana ci gaba da gyare-gayre a Majalisar Dattawa da ta Wakilai, lamarin da ya sa ’yan majalisar suka koma matsugunin wucin gadi.