✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ranar Hijabi: Kalubalen da mata masu hijabi suke fuskanta

Yau ita ce ranar sanya hijabi ta duniya, amma matan da ke sanya hijabi na fuskantar kalubale.

Ranar Hijabi ta Duniya rana ce da Nazma Khan, ’yar asalin kasar Bangladesh da ke zaune a Amurka ta kirkira a 2013.

An ware ranar 1 ga watan Fabrirun kowace shekara ce domin ta zama Ranar Hijabi ta Duniya, inda al’ummar Musulmi a kasashe sama da 140 suke bikin wannan rana ta hanyar karfafa wa mata gwiwa don amfani tare da sanya hijabi.

Sanya hijabi koyarwa ce ta addinin Musulunci wanda ya wajabta wa mata suturta jikinsu da tsiraici da kuma adonsu ga mazajen ba muharramanta ba, hakan ya sa wasu kasashen Musulumi irinsu Saudiyya, Iran, Afghanistan suke da dokokin da suka wajabta sanya hijab.

Dokokin kasashen duniya dai sun ba wa mutane ’yancin gudanar da addininsu ba tare da tsangwama ba, kuma yawancin mata Musulmi a sassan duniya su yi na’am da sanya hijabi.

Amma duk da haka, a wasu kasashe mata masu sanya hijabi na shan suka, tozarci, wulakanci, da muzgunawa musamman a kasashe irin su Amurka, Jamus, Faransa da sauran kasashen Turai.

Kalubalen da masu sanya hijabi ke fuskanta

Duk da cewa sanya hijabi abu ne mai kyau wajen suturta jikin mace, kuma ya samo asali ne a addinin Musulunci.

Amma duk da haka mata masu sanyawa na fuskantar kalubale iri-iri a duk lokacin da suka sanya shi a wuraren aiki, makaranta, kasuwanni da sauran wurare.

Dambarwar Hija a Kwara

A Najeriya, a baya-bayan nan a Jihar Kwara an tada hazo kan yadda wata makarantar sakandare ta Baptist da ke Ilorin, ta hana kafa dokar hana mata masu sanya hijabi shiga makarantar.

Wannan lamari ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar jihar da sauran Musulmin Najeriya, inda suke ganin babu adalci kan hukunci, saboda kundin tsarin mulkin ya ba wa kowane dan kasa damar yin addininsa da kuma da al’adarsa.

Firdausi Amusa

A ranar 16 ga watan Disambar 2017 irin haka ta faru da wata dalibar Jami’ar Ilorin, Firdaus Amasa da aka hana shiga wurin bikin yaye daliban Makarantar Lauyoyi ta Najeriya da ke Ilori.

Shi wannan lamari na ta ya yamutsa hazo, wanda aka dinga dauki-ba-dadi har daga bisani aka aminta aka bar ta ta ci gaba da sanya hijabinta.

Daga karshe dai, bayan an kai gwauro an kai mari, ta yi nasara aka kuma mika mata shahadarta da kammala makarantar da kuma sahale wa mata Musulmi sanya hijabi tare a kayan lauya.

Faransa ta haramta sanya hijabi

An jima ana dauki ba dadi a kasar Faransa kan hana mata sanya hijabi a bainar jama’a.

A kan haka ne har a wani lokaci gwamnatin kasar ta sanya tara a kan duk macen da ta sanya hijabi a bainar jama’a.

Yin hakan, a cewar gwamnatin ta Faransa, wani mataki ne na neman takaita tsattsauran ra’yi.

Filin jirgin Amurka

Mata Musulmi da dama sun sha fuskantar kalubale da tsangwama a saboda sun sanye da hijabi, musamman a kasashe irin Amurka da Faransa a shekarun baya da suka shude.

Wata mata mai suna Fatima Altakrouri wadda aka haifa a Arewacin yankin Texas na kasar Amurka, ta bayyana yadda ta taba fuskantar tsangwama a filin tashin jirage na Texas.

“An hana ni shiga jirgi saboda ina sanye da hijabi, abin ya yi matukar ba ta min rai, an keta min haddi,” kamar yadda ta bayyana wa kafar yada labarai ta CNN.

Wannan ba ita ce kadai macen da ta taba fuskantar matsala a dalilin saka hijabi ba, dubban mata da ke rayuwa a kasashen turai sun fuskanci ire-iren wadannan kalubale.

Sai dai shin wace hanya ya kamata a bi don ganin an kawo karshen irin kalubalen da mata masu sanya hijabi ke fuskanta, tun daga nan gida Najeriya zuwa sauran kasashen duniya baki daya?