Gwamnan Jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya, ya nemi sauran kabilun da ke jiharsa da su yi koyi da Hausawa wajen karrama yarensu.
Yahaya ya kalubalanci kabilun da ke jihar a wajen biki taron ranar Hausa ta Duniya da aka gudanar ranar Alhamis a Gombe.
- Tattalin arzikin Najeriya ya karu a rubu’i na biyu na 2021 —NBS
- ‘Dalilin da Najeriya za ta mallaki hannun jari a Matatar Dangote’
Ya ce yaren Hausa harshe ne da kusan ko ina ana amfani da shi a duniya.
Gwamna Yahaya, wanda kwamishinan yada labarai da al’adun gargajiya Julius Ishaya ya wakilta, ya ce wannan taro ya zama zakaran gwajin dafi kasancewar sa karo na farko.
Ya ja hankalin sauran kabilun jihar yaruka a jihar da su samar da wata rana ta musamman don karrama yarensu kamar yadda al’ummar Hausawa ke yi.
Da ya ke jawabi, Sarkin Hausawan Afirka kuma Sardaunan Agadas, Dokta Abdulkadir Koguna, cewa ya yi yaren Hausa shi ne na 15 mafi daukaka a fadin duniya kuma kullum cinye wasu yaruka ya ke kara yi.
Dokta Koguna, ya ce saboda daukakar da harshen ya ke da shi ya sa a kasar Saudiya ma an taba yin hudubar sallar Idi da shi.
A cewarsa, yunkurin mutunta harshen Hausa ya sa kwararru suka zauna suka ware ranar 26 ga watan Agusta ta zama ranar Hausawa ta duniya.
Ya kara da cewa duk da yadda harshen Hausa ya daukaka ana musgunawa al’ummar Hausawa musamman da suke yankin arewa inda ya ce karfi da yaji ake so sai anga bayan yankin.
Kazalika, ya yi kira ga gwamnati da hukumomi da cewa a gaugauta daukar mataki don kar a kuresu lamarin ya kai su ga bango.
Wani masanin adabi kuma malami a jami’ar gwamnatin tarayya ta Kashere, Dokta Babayo Sule, ya ce Bahaushe mutum ne mai al’ada da addini tun kafin zuwan turawa wanda har turawa suka zo ba su canja musu al’adunsu ba.
Dokat Babayo, Sule, ya ja hankalin al’ummar Hausawa da cewa yanzu sun fara juya al’adunsu baya don haka su hankalta su dawo da su.
Ya kuma shawarci al’ummar Hausawa da cewa kamata ya yi bikin ya zama na kwanaki uku ba kwana daya ba don gudanar da laccoci da mukalu kan asalin tarihin Hausawa.
Da yake jawabin godiya, mai masaukin baki, Sarkin Hausawan Gombe Alhaji Nasiru Inuwa Danmalam, ya yaba wa al’ummar Hausawan duniya musamman wadanda suka turo wakilansu don halartar taron.
Danmalam, ya ce kasancewar wannan taro shi ne na farko kuma ya zama abun buga misali, nan gaba taron da za a yi a Gombe sai ya fi haka armashi.
Aminiya ta ruwaito cewa, an gudanar da taron a Kofar Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar, kuma ya samu halartar wakilin Sarkin Hausawan Sudan da na Kamaru da na kasar Amurka da na sassan kasar nan.