A kowace ranar 26 ga watan Agusta ne wasu kungiyoyi da kafafen sadawar zamani daban-daban suke gudanar bukin ranar Hausa ta duniya, wanda a bana ya kasance karo na biyu da aka shirya irinsa a bainar jama’a, sabanin yadda aka faro shi kuma ya takaita a shafukan sada zumunta, tun bayan da wani dan jarida ma’aikacin BBC Hausa mai suna Abdulbaki Jari ya kirkiro da ita a shekarar 2015.
A shekarun baya babu irin wannan rana da za a ce al’ummar Hausawa sun ware suna tunatar da juna kyawawan al’adunsu, gudunmawar da harshen Hausa ke bayarwa ga ci gaban rayuwa da sauransu.
- Abin Da Ya Sa Tashe-Tashen Hankula Suka Ki Karewa A Najeriya
- Kamata ya yi a mayar da Hausa yaren Kasa a Najeriya – Farfesa Dangambo
Kawai dai suna zaune ne kara zube, da takamar kasancewarsu masu magana da babban harshe mafi saurin yaduwa a Najeriya, kuma daya daga cikin manyan harsunan Afirka.
– Makon Hausa
Amma a gefe guda yaya manyan masu ilimi da manazarta daban-daban da ake da su suka lura da kalubalen da al’ummar Hausawa da shi kansa harshen Hausa ke fuskanta, don samar da lokacin da ya dace a yi nazarin cigaban da harshen ya samar da matsalolin da yake cin karo da su, a jiya da yau?
Ina iya tunawa tun a shekarun baya wasu jami’o’i kan ware tsawon wasu kwanaki ana gudanar da tarukan kara wa juna sani, wanda ake kira da Makon Hausa, inda ake gabatar da laccoci da makalu daga manyan masana.
Kamar misalin Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato da Jami’ar Bayero da ke Kano, da sauran manyan cibiyoyin ilimi da ke da sashin nazarin harsuna.
– Ranar Hausa
Tun bayan da aka kirkiro da bukin wannan rana kimanin shekara biyar da suka gabata, bukin ya fi karkata ne a shafukan sa da zumunta musamman ma shafin Twitter inda ake da gungun Hausawa ’yan boko da masu ilimi da kishin ganin an samar da cigaba a bangarorin rayuwa daban-daban, da niyyar hada kai tsakanin masu magana da harshen Hausa da tunatar da su muhimmancin kiyaye al’adu da harshen Hausa.
A lokacin akan mayar da ranar ta zama ranar amfani da Hausa wajen rubuce-rubuce a shafin na Twitter, da tattaunawa kan wasu kalmomi na Hausa ko ma’anonin karin maganar Hausawa da azancin da ke kunshe a cikinsu.
Hakan yana taimakawa matasa ’yan boko musamman wadanda ke ganin amfani da Hausa wajen rubutu a shafukan sa da zumunta kauyanci ne da rashin wayewa, babu ma kamar a manhajar Twitter.
Hakan ya tilasta wasu da ba su yi zurfi a bokon ba su yi ta kokawa da turancin a kokarin ganin sun isar da sakon da suke son isarwa, ko don su ma a dauke su a cikin wayayyu.
Wannan dabi’a ta ’yan Twitter ita ce ta rage masa karsashi a tsakanin matasan Arewa, abin da kuma ya kara bai wa Facebook karbuwa sosai ke nan, saboda yadda ya kasance tamkar jakar dan magori, ta kunshi kowanne irin mutum da ra’ayoyi iri daban-daban damar baje kolinsa.
Wannan daya ne daga cikin dimbin matsalolin da harshen Hausa da al’ummar Hausawa ke fuskanta.
– Hausawa sun guji Hausa
Ba tun yau ba malamanmu da masharhanta ke kokawa da yadda ’ya’yan Hausawa na asali ke nisanta kansu da harshen da al’adunsu, wadanda akasari tushensu daga addinin Musulunci ne, ko kuma addinin ne ya kara gyara su.
Da wuya ka ga dan boko bahaushe yana karanta littafin Hausa ko jaridar Hausa, ballantana wakokin gargajiya na Hausa in ba wakokin soyayya na zamani ba.
Ko da kuwa ka gan shi cikin sutura irin ta Hausawa, bai cika son nuna kansa a matsayin bahaushe ba, sai idan hakan zai dace da wani burinsa ko ra’ayinsa.
Wannan shi ya sa kasuwar jaridun Hausa ke kara baya, kasuwar adabin Hausa wacce a da ta yi shuhura, saboda hazikan marubuta da suka rika fitar da rubuce-rubuce da littattafai, yanzu ita ma ta mutu.
Matasan marubuta da a yanzu suke tasowa a kafafen sa da zumunta rashin gogewa da lakantar harshen ya sa rubuce-rubucen nasu ba sa samun tasirin da na baya suka yi.
Hatta shafukan watsa labarai da ake da su na Hausa a wasu kafafen sa da zumunta, ba a cika daukar su da muhimmanci ba, musamman daga bangaren hukumomi da manyan ’yan siyasar Arewa da makamantansu, don haka babu abin da suke samu ballantana su inganta aikin ya kai darajar na turanci mallakin ’yan Kudu.
– Adabin Hausa na cikin tasku
Hajiya Mairo Muhammad Mudi, wata ’yar jarida kuma marubuciya da ke da mallakin kamfanin jarida na Zuma Times ta taba koka min kan irin abin takaicin da masu shafukan labaru na Soshiyal Midiya suke fuskanta, inda take cewa, a kashin gaskiya, aikin jarida musamman na yanar gizo, yana ganin wulakanci da takaici.
Babban kalubale shi ne na rashin kudin tafiyarwa. Mutanenmu na Arewa da muka tsaya tsayin daka wajen kare martabarsu da karrama su ba sa ganin kimar abin da muke yi.
Manyanmu da ’yan siyasarmu sun gwammace su kyautata wa ’yan jaridar Kudu bisa ga na Arewa wadanda in sun tashi cin mutuncinmu ba sa rabe dayan biyu, kudin goro suke yi mana.
Suna amfani da kafafensu wajen durkusar da namu manyan da yankinmu na Arewa, amma kuma su ne abin tallafawa.
Mu sun raina mu sun fi ba su daraja. Jaridun kudu na ci musu mutunci mu muna kare su, amma duk da haka su suke tallafa wa, mu kuma ko oho, suna watsar da mu!
Bugu da kari, masu bibiya ba kowa yake da fahimta da tarbiyya ba, wasu da sun karanta labari in bai masu dadi ba sai su yi ta aiko da kalamai na cin mutunci ko su dankara muku ashar. Malam Bahaushe kenan!
– Abin takaici
A yayin da wasu kabilun ke shigowa Arewa suna cin abinci da samun alheri da harshen Hausa, mu namu ’yan na gada kyamar harshen suke yi.
Ta kai za ka je kamfanonin tallace-tallace da kafafen watsa labarai ka ga wai kabilu ne suke gudanar abubuwan da ake yi da Hausa, ko kuma ka ga wanda ba bahaushe ba ne ke shugabantar sashin Hausa a wani babban gidan rediyo ko talabijin, kuma sai yadda ya ga dama ake yi.
Wani lokaci ka ji ana tallata wani kayan sayarwa da Hausa, amma kamar mutum ya yi amai; Ko ka ga allon talla a kan hanya an rubuta shi da wata bagwariyar Hausa.
Duk kuma an zuba ido babu wata babbar murya da ke fitowa tana tsawatarwa.
Hatta a wasu manyan makarantu na duniya, inda ake koyar da harshen Hausa, sai ka je ka ga wadanda ke koyar da Hausa kabilu ne da babu abin da ya hada su da harshen Hausa, in ba zaman wuri daya ba.
Mutum ya ziyarci ofisoshin jakadancin Najeriya inda ake bukatar masu tafinta da sauran ayyuka da suka danganci Hausa, sai ya zubar da kwalla.
A wata tattaunawa da muka yi da wani fitaccen masanin harshen Hausa, kuma Shugaban Kungiyar Marubuta Wakokin Hausa, Farfesa Suleiman S. Mai Bazazzagiya, ya shaida min cewa, harshen Hausa na daga cikin harsunan da suka fi saukin samar da damar ayyukan yi, musamman ayyukan da suka shafi koyarwa, aikin fassara, bankuna da sauransu, inda ake bukatar wanda yake da wata shaidar karatu a Hausa, amma sai ka ga kalilan ne suke samun shiga.
A takaice, ina mai taya al’ummar Hausawa murna da samun wannan rana da za ta bayar da damar tattauna irin wadannan kalubale da ba da shawarwarin yadda za a shawo kansu.
Sannan kuma ya zama rana ce ta farkar da matasan Hausawa, da manyan jami’an gwamnati su gane cewa, kayan ado ba ya rufe katara!
Lallai ne sai mun daraja kanmu a matsayin Hausawa da harshenmu na Hausa kafin wasu su daraja mu.