Kungiyar Masu Gidajen Burodi ta Najeriya (PBAN) ta ce ta kammala dukkan shirye-shiryen fara yajin aikin kwana hudu daga ranar Alhamis, 21 ga watan Yulin 2022, a duk fadin kasar.
Masu sana’ar dai za su tsunduma yajin aikin ne don nuna damuwarsu kan yadda tsadar fulawa da sauran kayan hadi ke kara tagayyara sana’arsu.
- Dalilin da manyan kungiyoyin Turai ba sa son sayen Ronaldo
- Gudaji Kazaure: Ina nan tare da Buhari, duk da na bar APC
Shugaban Kungiyar na kasa, Emmanuel Onuorah da kuma mai magana da yawunta, Babalola Thomas, sun kuma roki Gwamnatin Tarayya da ta dakatar da cajinsu kaso 15 cikin 100 na fulawar da ake shigowa da ita Najeriya.
Sun kuma nemi Hukumar da ke Tabbatar da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta rage tarar N154,000 da take cin masu gidajen burodin da suka ki sabunta lasisin su a kan lokaci.
Kungiyar ta kuma roki gwamnati ta fara barin mambobinta su ci gajiyar rancen da Babban Bankin Najeriya yake ba kanana da matsakaitan sana’o’i.
“Yanayin da muke sana’a a Najeriya na tsadar kayayyaki ya kusa ya gurgunta masu sana’ar baki daya. Galibinmu asara kawai muke tafkawa, hakan kuma ba abu ne mai dorewa ba.
“Burodi daya ne daga cikin nau’ukan abinci mafiya aha da talaka da mai kudi ke amfani da shi. Saboda haka, ya zama wajibi gwamnatin Tarayya ta yi la’akari da wannan muddin tana so mu ci gaba da yin sana’a.
“A kokarinmu na tabbatar da ci gaba da ayyukanmu, mun yanke shawarar fara yajin aiki daga ranar Alhamis, 21 ga watan Yulin 2022, na tsawon kwana hudu, in kuma muka ga ba a yi komai ba, za mu tsawaita shi zuwa abin da hali ya yi.
“Mun yi amannar cewa yin hakan ne zai sa gwamnati ta faka ta fahimci halin da muke ciki da kuma yadda muka jima muna hakuri,” inji su.