Sergio Ramos ya bayyana aniyarsa na jinge takalamansa daga murza wa Spain leda, bayan tattaunawa da sabon kocin tawagar ’yan wasan, Luis de la Fuente, wanda ya ce ba ya cikin tsarinsa.
Dan wasan mai shekara 36 a duniya wanda ya lashe Kofin Duniya a 2010, bai sake buga wa kasarsa wasa ba tun 2021.
- An kwato makamai fiye da dubu 10 sa’o’i kafin zabe
- NAJERIYA A YAU: Yadda Bangar Siyasa Ka Iya Dagula Lissafi A Wannan Zabe
Sai dai ya so a ce an sake ba shi dama don nuna wa duniya cewar har yanzu da sauransa.
Amma ya ce, “Lokaci ya yi da zan yi bankwana da tawagar kasata.
“Yau (Alhamis) na samu kira daga sabon kocinmu, inda ya ce ba na daga cikin tsarinsa duk da irin kokarin da nake yi a yanzu.”
Hukumar Kwallon Kafa ra Spain (RFEF) ta tabbatar da tattaunawar da ta gudana tsakanin Sergio Ramos da sabon kocin, amma ba ta karin haske kan abin ya gudana ba.
Ramos ya buga wa Spain wasansa na karshe a share fagen Kofin Duniya a wasan da suka doke Kosovo da ci 3 da 1.
Tsohon dan wasan na Real Madrid, ya sauya sheka zuwa PSG a 2021, inda ya shafe kusan shekarar yana fama da rauni.