✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadaniyya: Kyautar musamman ga mai azumi (2)

9.    Mutanen da azumi bai wajaba a kansu ba:a.    Kafirci: Azumi bai wajaba a kan kafiri.b.    karamin yaro: Azumi bai wajaba a kan yaro har…

9.    Mutanen da azumi bai wajaba a kansu ba:
a.    Kafirci: Azumi bai wajaba a kan kafiri.
b.    karamin yaro: Azumi bai wajaba a kan yaro har sai ya balaga; kuma ana gane balagar yaro ta hanyoyi uku:
I.    Fitar maniyyi ta hanyar mafarki ko wata hanya daban.
II.    Tsirar gashin hammata ko na gaba.
III.    Cika shekara 12 ko 15 ga mata ko 15 zuwa 18 ga maza. Ga mata da karin ganin jinin haila.
c.    Hauka: Babu azumi a kan mahaukaci har sai ya warke.
d.    Tsoho ko tsohuwa tukub, wanda bai iya bambance wadanda ke zuwa wurinsa. Irin wadannan tsofaffi sai su ciyar da Mudun Nabiyyi guda a mazaunin azuminsu kowace rana har a gama azumin.
e.    Haka ma hukuncin yake ga wanda ba zai iya azumi ba, koda lokacin sanyi ne ko ruwa saboda ciwon yunwa ko ciwon kishin ruwa, kuma ba a tsammanin zai warke, shi ma zai ciyar da Mudun Nabiyyi kowace ranar azumi.
10.    Wadanda azumi ya wajaba a kansu:
a.    Musulmi namiji da Musulma mace baligai.
b.    Mai hankali, azumi wajibi ne a kansa.
c.    Lafiya: Don mara lafiya azumi bai wajaba a kansa, sai ya warke.
d.    Da kuma tsarkakuwa daga jinin haila da na biki ga mata.
11.    Wadanda azumi bai wajaba a kansu ba, amma dole su biya:  
a.    Matafiyi idan ya sha azumi a cikin tafiya dole ya biya.
b.    Mara lafiya yana iya shan azumi duk lokacin da ya warke sai ya biya abin da ya sha.
c.     Mai haila ba azumi a kanta, amma in ta yi tsarki za ta biya abin da ta sha, kuma idan mai haila ta dauki azumi sai jini ya zo mata kafin rana ta fadi azumin ya baci. Haka idan jinin haila ya dauke mata da rana a Ramadan ba azumi a kanta a sauran wannan yini, sai dai za ta rama azumin wannan rana da sauran kwanakin da ta sha. Kuma idan jinin ya dauke kafin fitowar alfijir koda da mintuna kadan ne kafin fitowar alfijir din to azumi ya wajaba a kanta.
karin bayani: Shi ma jinin haihuwa kamar jinin haila ne cikin dukkan hukunce-hukuncensa.
d.     Mace mai shayarwa idan ta ji tsoron danta ba zai samu nonon da za ta shayar da shi ba sai ta ci abinci, to tana iya cin abinci  bayan azumi ya wuce sai ta rama gwargwadon abin da ta sha. Haka kuma hukuncin yake ga mace mai ciki idan ta ji tsoron abin da ke cikinta, ita ma tana iya shan azumi, amma wajibi ne a kanta ta biya gwargwadon abin da ta sha bayan ta haife cikin nata.
e.     Wanda wani dalili ya sa ya sha azumi kamar ya yi kokari don kubutar da wani rai da zai halaka saboda gobara ko nutsewa a ruwa, sai a kokarin tserar da wadannan mutane ya sha azumi, to bayan azumin zai rama gwargwadon abin da ya sha.
12.    Buda-Baki:
Buda-baki shi ne mai azumi ya ci wani abu lokacin da ya tabbatar rana ta fadi. Yin haka yana daga cikin abin da ake so, saboda Annabi (SAW) ya ce: “Al’ummata ba za ta gushe tana samun nasara ba matukar tana gaggauta buda-baki.” Imam Buhari ya ruwaito Hadisin. Kumaana buda-baki ne da kayan marmari kamar lemu da ayaba da abarba da dabino danye ko busasshe da sauran kayan marmari. Idan kuma ba a samu daya daga cikinsu su ba, sai a yi buda –baki da ruwa. Manzon Allah (SAW) ya kasance yana buda-baki kafin ya yi Sallar Magriba, kuma yana yin buda-baki da kayan marmari ko dabino, kamar yadda Imam Tirmizi ya ruwaito.
13.    Addu’ar Buda-Baki:
“Ya Allah! Gare Ka na yi azumi, kuma da arzikinKa na yi buda-baki, Ya Ubangiji! Ka karbi wannan azumi da na yi.”
14.    Wadanda ake karbar addu’o’insu:
Daga cikin wadanda ake karbar addu’o’insu akwai mai azumi yayin buda-baki. Saboda Annabi (SAW) ya ce: “Mutum uku ana karbar addu’o’insu: Shugaba mai adalci da wanda aka zalunta da mai azumi lokacin buda-baki.”
15.    Ladar wadanda suke ciyar da mai azumi:
Ba mai azumi abin buda-baki yana daga cikin sadakoki masu lada da yawa, saboda Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya ciyar da mai azumi yayin buda-baki, to za a ba shi  ladar mai azumin ba kuma tare da an rage wa mai azumin ladarsa ba.” Imam Tirmizi ya ruwaito shi.
16.    Da’ifan Hadisai a kan azumi:
Daga cikin Hadisan da aka dangantawa ga Annabi (SAW) da wadansu malamai suke gani da’ifai ne akwai:
a.    “Ku yi azumi za ku samu lafiya.”
b.     “Azumin watan Ramadan yana rataye a tsakanin sama da kasa, har sai mutum ya ba da Zakkatul Fidiri.”
Wadansu malamai suna ganin cewa irin wadannan Hadisai suna daga cikin Hadisan kwadaitarwa da kuma kwadaitarwa don kada a yi sake.
17.    Sallar Tarawihi:
Sallar Tarawihi tana daga cikin sallolin nafila da ake yi a cikin azumi, kuma abin da ya sa ake kiranta Tarawihi shi ne saboda zaman da ake yi a kowane raka’a biyu a yi sallama, wato an dauke wannan kamar zaman hutu ke nan. Yin Sallar Tarawihi Sunnah ce, yawan raka’o’inta kuma 13 duk da Shafa’i da Wutiri. A wata ruwayar kuma an ce raka’a 11 ne duk da Shafa’i da Wutiri, saboda A’isha (RA) ta ruwaito cewa: “Annabi ba ya kari a kan raka’a goma sha daya da yake yi cikin dare a Ramadan ko ba a Ramadan ba.”
18.    Nafilolin dare a gima na karshen Ramadan:
Daga A’isha (RA) ta ce: “Annabi (SAW) ya kasance idan goman karshe na Ramadan ya zo, to ba ya barci, sai ya tada mutanen gidansa maza da mata ya ja dantse a dukufa ga nafilfili har karshen watan Ramadan.” Imam Buhari ya ruwaito.
19.    Sahur da ladarsa da lokacin yinsa:
Sahur shi ne cin abinci a karshen dare kafin fitowar alfijir da niyyar ibada. Sahur Sunnah ne mai karfi don Annabi (SAW) ya ce: “Bambancin azuminmu da azumin Ma’abuta Littafi cin abincin Sahur.” Imam Muslim ya ruwaito. Game da ladarsa Annabi (SAW) ya ce: “Ku yi Sahur, hakika akwai albarka a cikin yin Sahur.” Muslim ya ruwaito. Game da lokacin yin sa an samu Hadisi daga Sabit (RA) ya ce: “Mun yi Sahur da Annabi (SAW) sai ya tashi zai yi Sallah, sai na tambaye shi, ayoyi nawa mutum zai iya karantawa tsakanin kiran Sallah da barin Sahur? Sai Annabi (SAW) ya ce: “Tsakanin kiran Sallah da barin Sahur mutum zai iya karanta ayoyi hamsin.” Imam Buhari ya ruwaito.
20.    I’itikafi:
I’itikafi shi ne mutum ya zauna a masallaci don yin nafilfili da karatun Alkur’ani da addu’o’i domin neman dacewa daga Allah duniya da Lahira. Shi Sunnah ne da ake so a yi a goman karshe na watan Ramadan. Kuma an ce karancinsa kwana daya da yini, amma akasarinsa kwana uku. A wata ruwayar an ce karancinsa kwana uku, akasarinsa kwana goma har zuwa wata guda. Kowanne ka zaba cikin wadannan maganganu ya yi daidai.