✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadaniyya: Kyautar musamman ga mai azumi (1)

Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya isar da komai. Tsira da aminicin Allah su tabbata bisa Annabi Muhammad da bayinSa zababbu.Bayan haka, a yayin…

Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya isar da komai. Tsira da aminicin Allah su tabbata bisa Annabi Muhammad da bayinSa zababbu.
Bayan haka, a yayin da muka shiga goma na biyu na azumin watan Ramadan, ina mika wannan takaitacciyar wasika mai suna Ramadaniyya da na ciro hujjoji daga Littafin Allah da Sunnar Manzo (SAW0 da zantukan malamai a matsayin kyauta ga masu azumi. Allah Ya sa shi a mizanina na kyawawan ayyuka a gobe kiyama.
1.    A yoyin da suka yi magana kan azumi:
Allah Madaukaki Ya ce: “Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suke gabaninku, tsammaninku za ku ji tsoron Allah. Kwanuka ne kidayayyu. To wanda ya kasance daga gare ku majinyaci ko kuwa yana a kan tafiya, sai ya (biya) adadi daga wasu kwanuka na daban. Kuma a kan wadanda suke yin sa da wahala akwai fansa; ciyar da matalauci, sai dai wanda ya kara alheri, to shi ne mafi alheri a gare shi. Kuma ku yi azumin (da wahalar) ne mafi alheri a gare ku, idan kun kasance kuna sani. Watan Ramadan ne wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa, yana shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa. To wanda ya halarta daga gare ku a watan, sai ya azumce shi, kuma wanda ya kasance majinyaci ko a kan tafiya, sai ya biya adadi daga wasu kwanuka na daban, Allah Yana nufin sauki a gare ku, kuma ba Ya nufi tsanani gare ku, kuma domin ku cika adadin, kuma ku girmama Allah a kan Ya shiryar da ku, kuma tsammaninku, za ku gode. Kuma idan bayiNa suka tambaye ka daga gare Ni, to lallai Ni Makusanci ne. ina karba kiran mai kira idan ya kira Ni. Saboda haka su nemi karbawaTa, kuma su yi imani da Ni: tsammaninsu, su shiryu. An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima’i zuwa ga matanku, su tufa ne a gare ku, ku ma tufa ne a gare su, Allah Ya sani, lallai ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Saboda haka Ya karbi tubarku, kuma Ya yafe muku. To yanzu ku rungume su, kuma ku nemi abin da Allah Ya rubuta muku. Kuma ku ci ku sha har silili fari ya bayyana a gare ku daga silili baki daga alfijir, sannan ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhali kuna masu I’itikafi a cikin masallatai. Wadannan iyakokin Allah ne: don haka kada ku kusance su, kamar haka ne Allah Yake bayyana ayoyinSa ga mutane: tsammaninsu, za su yi takawa.” (k:2:183-187).
2.    Hikimar  wajabta yin azumi:
Mu fara da sunan azumi wato Ramadan. Ramadan suna ne na watan tara daga cikin watannin Musulunci, kuma shi ne watan da Allah Ya ambace shi karara. Hikimar da ta sa aka wajabta mana azumi don tsarkake rai ne da sanya masa tsoron Allah don ya samu dacewa gobe Lahira.
3.    Ladubba wajibabbu ga mai azumi
a.    Wajibi ne mai azumi ya tashi da niyyar cewa azumi ibada ce cikin maganganunsa da aikace-aikaccensa.
b.    Ya nisanci abubuwan da aka haramta a maganganu da ayyukansa, kuma ya tsare ganinsa da jinsa da tafiyarsa daga haramtattun abubuwa. Wadannan wajibai ne ga mai azumi ya kiyaye su idan yana so azuminsa ya karbu a wurin Allah.
4.    Abubuwan da ake so ga mai azumi
a.    Jinkirta yin sahur.
b.    Gaggauta yin buda-baki.
c.    Yawan karatun Alkur’ani Mia girma.
d.    Yawaita addu’o’in alheri.
e.    Yawaita sadaka da kyauta.
f.    Yawaita ambaton Allah da tsarkake Shi.
5.    Falalar watan Ramadan:
a.    A cikinsa aka saukar da Alkur’ani. Allah Ya ce: “Watan Ramadan ne da aka saukar da Alkur’ani a cikinsa.”
b.    Ana gafarta zunubi a cikinsa, Annabi (SAW) ya ce: “Wanda ya yi azumin watan Ramadana yana mai imani da kyautatawa an gafarta masa abin da ya gabata na laifuffukansa.” Buhari ya ruwaito.
c.    Ana amsar addu’ar mai azumi, Annabi (SAW) ya ce: “Ana karbar addu’ar mutum uku: Mai azumi lokacin buda-baki da shugaba mai adalci da kuma wanda aka zalunta.”
d.    Daren Lailatul kadari, Allah Madaukaki Ya ce: “Daren Lailatul kadari ya fi wata dubu wajen alheri.”
e.    Ana daure shaidanu, saboda Annabi (SAW) ya ce: “Idan Ramadan ya zo ana daure shaidanu kuma a bude kofofin Aljanna.”
6.    Ma’anar azumi:
Abin da ake nufi da azumi shi ne: “Kamewa da barin ci da sha da duk wani abu da zai shiga cikin mutum da saduwa da iyali daga fitowar Alfijir zuwa faduwar rana.” Yin haka yana daya daga cikin rukunan Musulunci biyar. Don haka wajibi ne a kan Musulmi da Musulma baligai masu hankali kuma suna da lafiyar da za su iya yin azumi su yi.
7.    Abubuwan da suka halatta ga mai azumi:
a.    Yin asuwaki da rana da itacen da ba ya da dandano, wato dadi ko zaki ko bauri da sauransu.
b.    Yin tafiya cikin azumi idan bukatar haka ta taso.
c.    Zuba ruwan sanyi a kai ko wanka da ruwan sanyi idan zafi ya yi yawa don mutum ya ji sanyi-sanyi.
d.    Kana iya cin abinci da daddare amma ban da rana.
e.    Kana iya shan abin sha na halal da daddare.
Kana iya saduwa da iyalinka da daddare cikin watan Ramadan amma ban da rana.
f.    Kana iya amfani da magani na shafawa, amma na sha said a daddare.
g.    Kana iya yin allura da rana idan ba ta da dandano, amma ta karin ruwa ba ta halatta da rana ga mai azumi. Dalili kuwa idan ciwo zai kai a kara wa mutum ruwa, to ya halatta ya sha azumi idan ya samu sauki sai ya rama.
h.    Shafa turare idan ba na hayaki ba ne.
i.    Sai tozali sai da daddare ba da rana ba.
8.    Abubuwan da suke karya azumi:
a.    Cin abinci ko abin sha da rana.
b.    Saduwa da iyali da rana.
c.    Fitar da maniyyi da rana yana karya azumi, sai dai in mafarki ka yi, to wannan kam azumi bai karye ba.
d.    Wanda ya kago amai da gangan, azuminsa ya karye. Amma idan ba da gangan mutum ya yi ba, kuma wani abu daga cikin aman bai koma ba, to azumin bai karye ba.
e.    Fitar jinin haila ga mace yana karya mata azumi.
f.    Fitar jinin biki yana karya azumi.