✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ramadan: Watan yafiya da tausaya wa jama’a

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, Mai girma da buwaya. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Annabin Tsira, Annabi Muhammad (SAW) da…

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, Mai girma da buwaya. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga Annabin Tsira, Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da sahabansa da matansa da duk wanda ya yi koyi da shi har zuwa tashin Alkiyama.

Bayan haka, ya ’yan uwa Musulmi! Ina yi wa kaina wasicci da kuma ku, kan mu ji tsoron Allah a cikin dukkan al’amuran da za mu yi.

Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: “Ya ku wadanda kuka yi imani! An wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta wa wadanda suka zo kafin ku, ana fatar ku ji tsoron Allah.”

Ya ’yan uwa masu albarka, ya zama wajibi ga Musulmi kada ya yi sakaci a lokacin da Allah Ya ba shi dama. Kada ya yi wasa da wannan damar a lokacin da zai samu dama ya yi ibada. Lallai mu zamanto masu rige-rige wajen aikata ayyukan alheri.

Allah Madaukakin Sarki Ya kwadaitar da mu kan mu yi rige-rige wajen aikata alheri. Yana cewa “Kan haka ne sai masu tsare su zuba tsere su yi rage-rige wajen aikin alheri.”

Haka Allah Yana cewa “Ku yi gaggawa wajen neman gafarar Ubangijinku da neman Aljannah wadda fadinta ya kai fadin sammai da kasai baki daya. An tanade ta ce ga masu takawa.”

Ya ku ‘yan uwa masu tsoron Allah! Allah Madaukakin Sarki ya fifita abubuwa a kan abubuwa, mutane a kan mutane, lokaci a kan lokaci, zamani a kan zamani, kowane abu akwai fiffiko a tsakani. Saboda haka wannan falala ce.

Daga lokutan da aka fifita akwai lokacin watan Azumin Ramadan.Ya ’yan uwa masu albarkar ga wannan lokaci na watan Azumin Ramadan ya zo, wannan wata ne mai albarka wata ne wanda yake zama kamar rana ce a cikin taurari.  Wata ne da Allah Madaukakin Sarki Ya saukar da Alkur’ani a cikinsa.  Allah Yana cewa “Watan Ramadan wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa, akwai shiriya da kuma fayyacewa a tsakanin gaskiya da karya.”

’Yan uwa masu albarka wannan wata ne da Allah Ya wajabta mana azumi ba mu kadai ba, Ya wajabta wa duk mutanen da suka zo kafin mu. Allah Madaukakin Sarki Ya wajabta musu yin azumi, amma yaya suke yi wannan bai shafe mu ba.

Wannan wata ne na tuba, wata ne na gafara wata ne da yake kankare wa mutane zunubai. Hadisin Abu Huraira (RA) yana cewa Manzon Allah (SAW) ya ce a Sallar Biyar, wato tsakanin Sallah da Sallah da tsakanin Juma’a zuwa Juma’a da tsakanin Ramadan zuwa Ramadan ana gafarta wa mutum. Wallahi ban da Musulmi babu wanda yake samun wannan garabasar. A ce tsakanin Sallah da Sallah duk abin da ka yi, idan ka zo ka yi Sallah an yafe maka. Tsakanin Juma’a zuwa Juma’a idan ka zo ka yi an yafe maka, tsakanin Ramadan zuwa Ramadan abin da ka yi an yafe maka, idan ka nisanci miyagun ayyuka.

Babu shakka watan azumi wata ne na lada da gafara. Ke nan sai mu yi koyi da yadda Allah Madaukakin Sarki Yake gafarta mana, Yake yafe mana mu ma mu yafe wa ’yan uwanmu wadanda suka yi mana laifi, ba su sani ba. Mu yafe wa wadanda suka yi mana laifi da saninsu. Mu yafe wa wadanda suka yi mana laifi bisa kuskure.  Domin da wannan ne za ka zamanto ka yi wa sauran mutane fintinkau a ranar tashin Alkiyama.

Idan za ka samu wanda ya saba yi maka laifi ka fada masa ka ce saboda falalar wannan wata na Ramadan na yafe maka laifin da ka yi mini har abada.

Idan da Musulmi za su yi haka da mun tashi daga matsayinmu na Musulmi mun fara komawa matakin zama mumunai. Amma har yanzu muna nan a Musulminmu. Saboda idan an yi maka laifi za ka ce sai ka rama. To bai kamata ba, ya kamata mu yi koyi da wannan koyarwa da Allah Madaukakin Sarki ya sanya mana. Domin watan azumi an sanya shi ne don ya koyar da mu irin wadannan abubuwa. Kada ka damu da girman laifin da aka yi maka, ka dubi girman wanda za ka yafe dominSa. Kada ka damu da girman laifin da aka yi maka, idan aka yi maka laifi komai girmansa  ka kalli girman Allah ka yafe wa wanda ya yi maka wannan laifi.

Allah Yana cewa: “Shin ku ba kwa son Allah Ya yafe muku ne?  Idan aka yi wa mutum laifi ya yafe, zai ga irin sakamakon da Allah zai ba shi.

Saboda haka jama’a ku yi yafiya a tsakaninku da ’ya’yanku da matayenku da abokan sana’arku da abokan huldarku ku yafe musu.

Allah Ka shaida duk wanda ya shaida ya yi mini wani abu ni dai na yafe masa. Ko na sani ko ba sani ba, har wadanda suke cin namana. Kuma ina rokon Allah Ya gafarta musu.

Manzon Allah (SAW) ya bayyana cewa duk mutumin da ya tashi ya yi azumin watan Ramadan yana neman yardar Allah da ikon Allah, ya yarda da Allah ne Ya yi masa umarni, yana neman ladan Allah, ya yarda zai ba shi lada. Allah Madaukakin Sarki Ya ce za a yaye masa zunubansa baki daya.

Idan watan azumi ya kusa Ma’aiki (SAW) cewa yake yi, “Ya kai mai neman alheri! Zo ga alheri nan ya zo maka. Ya kai mai neman shirri an durkusar da kai, an dakatar da kai a kan wannan shiri naka”. Sannan yake cewa Allah Yana da wadanda yake ’yantawa daga cikin wuta. Wannan kowane dare na Ramadan ne. Allah Ka sa dukkan bayinka wadanda suka zo wannan Sallah da wadanda ba su zo ba, Allah Ka sa muna daga cikin wadanda za a ’yantar.

Wannan wata ne na albarka wata ne da ake bude kofofin Aljanna ake rufe kofofin wuta ake daure kangagararrun shaidanu. Allah Ka bude mana kofofin Aljanna.

Wata ne na hakuri, hakuri kuma yana bayyana ne balo-balo. Domin hakurin ne zai hana mutum ci da sha da kallon abin da kake son ka kalla da jin abin da kake son ka ji na wake wake, amma a wannan lokaci na watan azumi za ka hakura ka bar wadannan abubuwa. Hakuri kuma ba ya da sakamako sai gidan Aljanna.

Allah Yana cewa zai cika wa wadanda suka yi hakuri ladansu ba tare da Ya yi musu hisabi ba, Allah Ka sa muna ciki. Watan azumi wata ne na addu’a domin addu’a tana karbuwa a lokacin azumin wata Ramadan, shi ya sa Allah Madaukakin Sarki da Ya yi maganar ayoyin Alkur’ani kan azumi a karshe sai Ya kawo cewa “Idan bayiNa suka tambaye ka game da Ni, to fa Ina kusa.” Saboda haka Allah Madaukaki Yana jin ka Yana ganinka, tambaye Shi abin da za ka tambaya zai ba ka. Saboda haka, mu dage mu yi ta yin addu’o’i a wannan lokaci na wata azumin Ramadan.

Har wa yau wannan wata, wata ne na baiwa da kyauta da kare kai daga abubuwan da ba su da kyau.

’Yan kasuwa watan da za ku samu alheri ke nan. Watan da za ku yi wa jama’a sauki, ku sayar musu da kayayyaki da sauki domin su samu damar jin dadin bauta wa Allah su samu lada, ku ma ku samu lada.

Sa’annan duk abin da ka san kana aikatawa na haram ka bar shi, don kada ya zama ka yi aikin banza kana azumi ana daukar ladan ana bai wa wadanda kake cuta, don haka jama’a a kiyaye da wannan.

A nan zan yi amfani da wannan dama in yi kira ga al’ummar Musulmi kan mu yi amfani da wannan wata na azumi mu yi ta rokon Allah, masifar nan da take ta damunmu musamman a Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna da Jihar Zamfara da Jihar Taraba Allah Ya yaye mana. Domin wannan masifa ta shafe mu baki daya. Babu abin da zai fitar da mu daga cikin wannan masifa sai addu’o’i saboda haka mu yi amfani da wannan dama mu yi addu’o’i Allah Ya yaye mana wannan masifa.

Har ila yau ina son in yi amfani da wannan dama wajen yin bayani kan abubuwan da zamu yi a wannan masallaci na Sultan Bello, a wannan lokaci na watan azumin Ramadan.

Gyara ne za mu yi, za mu tsananta tsaro a wannan masallaci, masu ababen hawa wuraren da za su zauna daban. Wararen masu babura daban.  Mun tanadi ’yan agaji da jami’an tsaron masallacin. Kuma za mu kara dauko jami’an tsaro daga waje wadanda za su taimaka mana wajen tabbatar da tsaro a wannan masallaci. Babu wani mai kayan sayarwa da za a bari ya shigo cikin harabar masallacin. Masu sayar da kaya su je can waje su sayar da kayayyakinsu. Don Allah jama’a su ba mu hadin kai kan wannan mataki da muka dauka.