Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta bayar da umarnin rufe gidajen gala a jihar, a shirye-shiryenta na tukarar watan azumin Ramadan.
Wannan na zuwa ne, biyo bayan wata ganawa da shugaban hukumar ya yi da jagororin kungiyar masu gidajen gala da ke jihar a ofishinsa.
- Gobara ta tashi a tashar wutar lantarki ta ɗan Agundi a Kano
- PDP ta yi Allah-wadai da sace dalibai 200 a Kaduna
A cewar shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, dokar za ta fara aiki ne daga ranar Lahadi har zuwa 1 ga watan Shawwal, wato ranar bikin karamar sallah.
El-Mustapha ya gargadi masu gidajen wasannin na gala da su guji karya doka domin duk wanda hukumar ta samu da laifin karya dokar, za ta dauki tsatstsauran mataki a kansa, ta hanyar soke lasisinsa.
El-Mustapha ya kuma gode wa shugabannin gidajen galar tare al’ummar Jihar Kano, dangane da hadin kan da suke bau wa hukumar a kowane lokaci.
Kazalika, ya ja hankalin al’ummar jihar cewa kofarsa a bude ta ke domin ba shi shawara ko sanar da hukumar duk wani al’amari da zai taimake ta domin samun nasarar ayyukan da ta sanya a gaba.