A halin yanzu al’ummar Musulmi a ko’ina a fadin duniya sun shiga watan azumin Ramadan, wanda ya sanya suka himmatu wajen gudanar da ibada tare da gudanar da ayyukan alheri iri-iri domin neman yardar Allah a wannan wata mai dimbin albarka.
Watan Ramadan wata ne da aka saukar da Alkur’ani a cikinsa, kuma a cikinsa ne ake samun Daren Lailatul Kadari, daren da ibadar da aka yi a cikinsa ya fi wanda aka yi na tsawon wata dubu. Kuma a goma na farkon watan rahama ake samu, a goma na biyu kuma gafara ake samu, a yayin da a goma na karshe ake samun ’yantawa daga wuta.
A kokarin da Musulmi suke yi na samun lada a wurin Allah a wannan wata mai alfarma, akwai taimaka wa masu karamin karfi da daukar nauyin tafsirai da ciyarwa da shirya buda-baki da zuwa Umara da karatun Alkur’ani da sauran ayyukan alherai masu yawa.
Sai dai kuma a cikin duk ayyukan alherin da za a gabatar babu kamar ciyarwa. Domin ko dabba aka ciyar ana samun lada, ballantana mutum. Shi ya sanya aka ce idan mutum ya ciyar da mai azumi koda da kwarar dabino ne zai samu lada, kwatankwacin ladar da za a ba mai azumin ba tare da an rage ladar mai azumin da ya ciyar ba.
Saboda haka ya kamata a himmatu wajen ciyar da bayin Allah masu azumi. Mabukata suna nan birjik a kewaye da mu. Ga ’yan gudun hijira nan a sansanoni da dama wadanda suke tsananin bukatar taimako. Wadansu ’yan gudun hijirar ba a sansanoni suke zaune ba, suna zaune ne a gidajen ’yan uwansu, da su da ’yan uwan nasu duk suna bukatar a taimaka musu, domin ’yan uwan nasu ba masu karfi ba ne. Sai kuma ’yan gudun hijira suka zo suka kara musu nauyi a gidajensu. Saboda haka suna bukatar a taimaka musu. Irin wadannan suna nan a unguwanni da dama a cikin garuruwan Arewa da dama.
Masu hali su daure su tausaya wa marasa hali, maimakon a tara abinci iri-iri a lokacin buda-baki. Ga farfesun kaza, ga na rago, ga na kayan ciki, ga abinci da nama zuku-zuku, ga koko da kosai, ga tsire, ga kayan marmari iri-iri da sauran abubuwa da dama wadanda ko rabinsu ba a iya cinyewa, karshenta ma sai dai a zubar saboda babu masu ci a kusa. Kamata ya yi a rage wasu abubuwan a yi amfani da kudin wajen taimaka wa mabukata da ke wasu wuraren.
Wadansu sukan shirya buda-baki su gayyaci abokansu da sauran mutane, hakan yana da kyau. Amma da za a samu mabukata a ba su kudi ko abincin su je su ciyar da iyalinsu da ya fi kyau, domin wadansu da aka gayyata sun bar iyalansu babu abin da za su ci, ga shi sun zo suna cin abinci har sun rasa yadda za su yi da shi, kuma suna jin kunyar diba su tafi da shi gida. Wadansu abokan da aka gayyata kuma masu hali ne, suna da abinci a gidajensu, amma saboda gayyatarsu da aka yi ba za su iya cin nasu na gida ba, ya zama barna ke nan.
Haka kuma maimakon a kwashi kudi a tafi Umara tare da iyali baki daya, kamata ya yi a daure a yi amfani da kudin nan wajen taimaka wa ’yan uwa da makwabta da marayu da gajiyayyu da sauran mabukata da ake da su birjik. Domin Allah bai wajabta wa mutum zuwa Umara duk shekara ba, amma Ya wajabta masa taimaka wa ’yan uwa da makwabta da marayu da gajiyayyu.
Idan har masu zuwa Umara suna yi ne domin neman yardar Allah, to taimakawa ita ce hanyar da za su bi su samu yardar Allah saboda sun bi umarnin Allah ba su bi son zuciyarsu ba.
A baya mai hali yana tafiya Umara ne shi kadai, amma yanzu ya zama gasa, sai mutum ya kwashi iyalinsa baki daya har da yara kanana a tafi Umara ba za a dawo ba sai bayan Sallah, kuma duk shekara sai ya yi haka, saboda kada a ce bana Alhaji ya gaza, ya kasa zuwa Umara! Alhali ga ’yan uwa da abokan arziki da makwabta da sauran mabukata ya bar su ya tafi yana yin abin da bai zama dole ba, kuma shi a ganinsa ta haka ne zai samu kusanci ga Allah.
Ba sai mutum ya je kusa da Ka’aba ne zai iya samun kusanci ga Allah ba, yana cikin gidansa ma zai iya samu. Wani kuma sai ya je Makka ga shi ga Ka’aba amma sai ya zama yana nesa da Allah, saboda ya tafi ya bar mutanensa a cikin wahala.
Marigayi Sheikh Usman Danf Fodiyo, bai samun yin aikin Hajji ba a rayuwarsa, amma sai ga shi Allah Ya daukaka matsayinsa. Har yanzu darajarsa sai karuwa take yi saboda ayyukan alherin da ya shuka. Haka shi ma marigayi Sarkin Zazzau Malam Ja’afaru Dan Isiyaku bai taba zuwa aikin Hajji ba, amma saboda adalcinsa da tsantseninsa har yanzu ana tunawa da shi.
Saboda haka ba wayo za a yi wa Allah ba, a kwashi kudi a tafi Umara ana shakatawa amma an bar bayin Allah cikin ukuba, kuma a ce ana so Allah Ya bayar da lada. Sai an aikata wajibi ne ake komawa mustahabbi. Amma idan aka aikata mustahabbi, aka bar wajibi akwai matsala. Allah Ya sa mu dace, Ya kuma ba mu ikon aikata abin da yake daidai ne.
Jama’a a daure a rika ciyar da mabukata a wannan wata mai alfarma da muka shiga domin akwai dimbin alheri tattare da haka. Kullum idan ka yi buda-baki, ka yi tunanin akwai wani da ya kai azumin, amma ba ya da abincin da zai ci. Ba lokacin azumi ba, a kowane lokaci ciyarwa tana da dimbin lada, amma a lokacin azumi ladan ya fi yawa.
Manzon Allah (SAW) yana cewa, “Imanin dayanku ba ya cika, sai ya so wa dan uwansa abin da yake so wa kansa.” Domin haka, yadda ba ka so ka kwana da yunwa ka yi kokarin ganin na kusa da kai da sauran mabukata ba su kwana da yunwa ba.
Babu shakka ciyarwa babban al’amari ne domin akwai dimbin lada, musamman a lokacin Ramadan. Allah Ya sa mu fi karfin zuciyarmu mu rika taimaka wa ’yan uwanmu.