Fadar Shugaban Kasa ta yi karin haske game da rahotanni da ke yaduwa a kasar kan cewa gobara ta tashi a cikinta.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ta ce ko kadan babu wata gobara da tashi a cikin fadar Shugaban kasar ta Aso Villa da ke birnin Abuja.
- An harbe ’yan bindiga hudu a Kaduna
- Sojoji sun fatattaki ’yan Boko Haram daga hanyar Damaturu zuwa Maiduguri
Sai dai ya ce tabbas wuta ta tashi a ranar Asabar 6 ga watan Maris wacce ta kone yayin da ke tsakanin katanga da kuma wayar da ta zagaye fadar Shugaban Kasar kuma ana tsammanin wani mai wucewa ne ya jefar da guntun karan sigari.
A yayin da yake bayar da tabbacin cewa babu rai ko daya da ya salwanta ballantana samun wanda ya ji rauni, ya ce Hukumar Kashe Gobara na ci gaba da bincike domin gano musabbabin tashin wutar.
Sanarwar ta ce, “jama’a a cikin Najeriya har da wajenta na ci gaba da nuna damuwa kan rahotannin tashin gobara a fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock Villa.”
“Ina so na yi karin haske da cewa babu wata gobara da tashi a Fadar Shugaban Kasar.”
“Da Yammacin Asabar 6 ga watan Maris, wuta ta shi wacce ta kona yayin da ke tsakanin waya da kuma katangar da ta zagaye fadar Villa daidai wurin da ke tsakanin fadar da kuma Barikin Soji na Asokoro, in ji Garba Shehu.
“Wutar kamar yadda ake tsammani ta tashi ne a sakamakon guntun karan sigari da wani mai wucewa ya jefar kuma a halin yanzu Hukumar Kashe Gobara na bincike a kan musabbabinta.”
“Babu asarar rai ko daya kuma babu wanda ya jikkata.”
“Muna mika godiya ga dukkanin ’yan Najeriya da suka nuna damuwarsu a kan lamarin.”