Najeriya na bin kasashen Jamhuriyar Nijar, Benin da Togo bashin kudin wutar lantarki da yawansu ya haura Naira biliyan 5.86 a iya shekara ta 2020.
Wani Rahoto da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta fitar ne ya nuna kasashen uku sun sha wutar lantarki ta Naira biliyan 16.31 a wannan shekarar.
- Na yi mamaki da na ji an ce Salman Rushdie bai mutu ba – Wanda ya caka masa wuka
- Sun shekara 8 suna gudanar da ofishin ’yan sanda na bogi a otel din Indiya
Rahoton ya ce daga cikin wannan adadi, sun biya Naira biliyan 10.45, sauran Naira biliyan 5.86. kuma Najeriyar na bin su bashi.
A cewar rahoton, NERC tana ba kasashen wuta ne ta bangaren da ke kula da kasuwanci na hukumar.
Su kuma kasashen na karba da kuma rarraba wutar daga hukumar ta hannun kamfanoninsu daban-daban.
Kamfanonin na kasashen su ne; Societe Nigerienne d’electricite (SNE) na Jamhuriyar Nijar, da Societe Beninoise d’Energie Electrique (SBEE) na Jamhuriyar Benin da kuma Compagnie Energie Electrique du Togo (CEET) na kasar Togo.