✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rage yawan masu tabin hankali

Dan kwallon Super Eagles da yanzu haka yake zaune a Rasha, Odion Ighalo a ranar Talatar da ta gabata ya bayyana yadda ya fuskanci barazanar…

Dan kwallon Super Eagles da yanzu haka yake zaune a Rasha, Odion Ighalo a ranar Talatar da ta gabata ya bayyana yadda ya fuskanci barazanar kisa shi da iyalinsa a wajen wadansu daga cikin magoya bayan kungiyar  Super Eagles jim kadan bayan an kammala gasar cin Kofin Duniya da aka yi a Rasha.

Ighalo wanda yake buga wa kungiyar kwallon kafa ta Changchun Yatai da ke Rasha wasa, ya ce ya kadu matuka game da yadda wadansu ’yan Najeriya suka rika aike masa da sakonnin zagi da batanci da barazanar kisa jim kadan bayan Ajantina ta fitar da Najeriya a zagayen farko a gasar cin Kofin Duniya a Rasha.

Ya ce ya san ya yi laifi bayan ya kasa zura kwallo a raga a yayin gasar, amma bai taba tunanin wani ko wadansu za su yi masa barazanar kisa saboda bai zura kwallo a raga ba.

“Yadda wadansu suka rika aika sakonnin batanci da zagi da na kisa ga iyalina, wadanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba, abin ya ba ni tsoro.  Hasali ma a wani lokaci sai da na yi tunanin daina buga wa Super Eagles kwallo”, inji shi.

Dan kwallon mai kimanin shekara 29 ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da kafar watsa labaran wasanni ta Kwese ESPN a garin Sfad da ke Tunisiya jim kadan bayan an kammala wasa a tsakanin kungiyar Super Eagles da Libya a ranar Talatar da ta wuce.

Najeriya ta lallasa Libya gida da waje, kuma Odion Ighalo ne ya zura kwallaye biyar a wasanni biyun.

Ighalo ya ce ya yi murna da ya taimaki Eagles wajen doke Libya a wasanni biyun da suka yi. Sannan ya yi murna da ya zura kwallaye shida a raga kawo yanzu a gasar neman zuwa gasar cin Kofin Afirka.

Sai dai jim kadan bayan kammala wasa a tsakanin Eagles da Libya a ranar Talatar da yawa daga cikin magoya bayan kungiyar Super Eagles sun yaba wa Ighalo, kuma sun ce sun yafe masa irin kura-kuran da ya yi a yayin gasar cin Kofin Duniya a Rasha.

Yanzu dai Ighalo yana daga cikin ’yan kwallon da kocin Eagles yake ji da su.