A ranar 21 ga Agustan nan ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya rantsar da sababbin ministocin da zai yi aiki da su a wa’adin mulkinsa na biyu, sai dai kuma a wannan karon ya fito fili ya bayyana musu cewa ba za su rika ganinsa kai-tsaye, babu shamaki ba.
Shugaba Buhari, tun a lokacin taron kara wa juna sani da aka shirya wa nadaddun ministocin ya bayyana musu haka, kuma ya sake nanata musu wannan maganar a ranar da ya rantsar da su.
Kamar yadda Shugaban ya nuna, ministocin ba za su iya ganinsa ba sai ta hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari, shi ne zai ba su dama su gana da Shugaban Kasa, idan ma wata takarda ce za su bai wa Shugaban Kasa sai dai su mika wa Abba Kyari ya kai masa.
Idan kuma wani batu ne da ya shafi Majalisar Zartarwa sai su tuntubi Sakataren Gwamnatin Tarayya shi ne zai yi wa Shugaban Kasa bayani. Wato dai yanzu Shugaba Buhari ganawa da shi bai da sauki ga ministocinsa ke nan, sai dai idan ana wani taro.
Wannan matakin da Shugaba Buhari ya dauka ya haifar da cece-ku-ce wanda ya sanya Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya fito ya yi karin bayani, inda ya nuna cewa wannan matakin ba sabon abu ba ne, tun a wa’adin mulkinsa na farko haka ake yi, yanzu an kara nanatawa ne kawai saboda ministocin da suke sababbi su san yadda abubuwa suke.
Sai dai kuma ga alama wannan bayanin da Garba Shehu ya yi, bai gamsar ba, domin masu sharhi suna ci gaba da tambayar cewa me ya sanya a farkon wa’adin Shugaba Buhari bai fito fili ya ce ministoci ba za su ganshi kai-tsaye ba sai yanzu, kuma idan ya bayyana haka a asirce ne a wancan lokaci me ya sanya a wannan karo ya bayyana wa ministocin a gaban duniya har sau biyu?
Babu shakka wannan matakin da Shugaba Buhari ya dauka ya rage darajar ministocinsa tunda an bayyana wa duniya cewa ba su da ikon ganin Shugaban Kasa kai-tsaye sai ta hanyar shamaki, wanda bai kamata ya kasance haka ba. Domin ministoci su ne masu zartar da ayyukan gwamnati don haka bai kamata a ce minista ba zai iya magana da Shugaban Kasa kai- tsaye ba sai dai ranar da ake taron Majalisar Zartarwa kawai.
Wannan matakin ya sanya ana ganin Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati Abba Kyari a matsayin ‘ka fi Mataimakin Shugaban Kasa,’ domin hada-hadar ofishinsa zai fi wanda ake yi a ofishin Mataimakin Shugaban Kasa. Hakan kuma na iya haifar da rashin jituwa a tsakanin Mataimakin Shugaban Kasar da Shugaban Ma’aikatan.
Haka kuma wannan cika wa ofishin Shugaban Ma’aikata aiki da aka yi zai jawo masa bakin jini, komai shi za a rika dora masa, domin ya zama kamar shi ne Shugaban Kasa. Kamar misalin kai ne da wuya, Shugaban Kasa shi ne kai wanda yake saman wuya, amma wuya ke juya kai yadda yake so.
Saboda haka a karkashin wannan tsarin sai Shugaban Ma’aikata ya ga dama zai bar minista ya gana da Shugaban Kasa, idan kuwa ya ce a’a, komai muhimmancin abin da ke tafe da shi dole haka zai hakura ya juya ya tafi. Wato dole sai minista ya rika fadanci da kamun kafa ke nan kafin ya samu damar ganawa da Shugaba Buhari.
Abin da yake daure wa mutane kai shi ne, a wannan karon Shugaba Buhari ya ce wadanda ya sani ne kawai ya dauko ya nada su ministocinsa, sabanin karo na farko da ya yi amfani da bayanansu da ya samu kawai. To shin su wadannan da ya ba su mukamin minista saboda ya sansu bai amince da su ba ne da ya sanya musu kandagarki wajen ganawa da shi?
Kamata ya yi a ce shugaba yana sanin halin da ministocinsa ke ciki a kowane lokaci ba tare da wani shamaki ba, domin akwai wani abu da minista ba zai so ya fada wa kowa ba, sai Shugaban Kasa kawai, amma a wannan tsarin dole sai minista ya yi wa Shugaban Ma’aikatan Fadar cikakken bayani idan ya gamsu sannan zai bari ya wuce ya ga Shugaban Kasa, idan bai yarda ba, yana iya yawo da hankalin ministan na tsawon lokaci ba tare da ya kyale shi ya ga Shugaban Kasar ba.
Hakan zai iya haifar da rashin jituwa a tsakanin Shugaban Ma’aikatan da ministoci, daga nan sai a samu matsala wajen aiwatar da muhimman ayyukan gwamnati, sai a bar talaka ya ci gaba da zama a cikin kuncin rayuwa ke nan, domin fadan manya zai shafe shi.
Saboda haka ya kamata Shugaba Buhari a matsayinsa na shugaban da talakawa tsantsa suka zabe shi, ya zama shugaba mai saukin gani, ba ma ga ministocinsa kawai ba har ma ga sauran jama’ar kasa.