Masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi a Najeriya sun alakanta rage mafi karancin makin cin jarabawar neman gurbi a manyan makarantu a kasar da faduwar darajar Ilimi.
A kwanakin baya ne hukumar shirya jarabawar shiga msnyan mkarantu (JAMB) ta sanar da rage mafi karancin makin neman shiga jami’a zuwa 140, na makarantun fasaha da kwalejojin ilimi kuma maki 100.
- Kashe-Mu-Raba: Ana Binciken Tsohon Shugaban Mexico
- Za mu kori duk wani azzalumin alkalin kotun Musulunci —Gwamnatin Borno
Shugaban Cibiyar Lissafi ta Kasa (NMC) Dokta Steve Olumaniyi ya bayyana cewa a ganinsa hakan ba zai shafi darajar Ilimi ba ko kadan, kasancewar kowacce jami`a na da tsarinta na bai wa dalibai guraben karatu.
Ya ce babbar matsalar ilimi a Najeriya ita ce rashin jagorori kwararru a dukkan matakan fannin, da suka gaza ciyar da shi gaba.
“Mu zargi gwamnati kan faduwar darajar Ilimi ba mizanin cin jarabawar JAMB ba, mu kuma kalli yadda yajin aiki ke kawo tsaiko ga karatun ’ya ’yanmu.”
A hannu guda wani mai bincike a cibiyar da ke Abuja ya ce duk da wannan sabon tsarin na JAMB din, jami’o’’i na da damar sauya makin daidai da yadda suke so, don haka wannan ba abin damuwa ba ne.
“Wasu fitattun jami`o`in sun sanya mafi karanacn makinsu ya dara na JAMB, misali yawanci sun sanya 180 a matsayin mafi karanci, haka su ma wasu makarantun fasahar da kwalejin ilimin”, in ji shi.
Sai dai shi ma ya amince da sanya maki 100 daga 400 ko 140 cikin 400 a matsayin abin da zai kawo nakasu ga bangaren ilimin.
Shugaban cibiyar Fafesa Stephen Onah ya ce hukumar ta rage ingantattun daliban da za su nemi gurabar a manyan makarantun bana, wanda hakan zai iya shafar ilimin a gaba a cewarsa.
“Ni ina ganin abin da ya fi muhimmanci shi ne rike darajar ilimi ta hanyar barin makarantun su zabi makin da suke ganin ya yi musu, musamman ga dalabai masu rauni “, in ji Onah.
Ita ma wata kungiya mai zaman kanta da ke bibiyar lamarin Ilimin Najeriya (SPEC) ta ce, ci gaba da rage makin babu abin da zai haifar wa kasar nan sai nakasu.
Shugabar kunngiyar, Vivian Bello ta ce abin damuwa ne yadda ake kara rage makin bayar da gurabaen a musamman ma na jami’o’i, domin hakan zai kara rage darajar su a idon duniya.
To sai JAMB din ta bakin kakakinta, Dokta Fabian Benjamin, ya ce ba ta taba tilasta wa mayan makarantu sanya adadin makin da za su yi amfani da shi ba a matsayin mafi karanci na bai-daya.
Ya ce ba su taba yin katsalandan din sanya wa makarantun wata ka’idar ba da guraben karatu ba, don haka suna iya sanya makin da suke so a matsayin mafi karanci.