Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Makarantun Gaba Da Sakandare (JAMB) ta dakatar da rajistar daliban da ke neman gurbin shiga jami’a kai-tsaye (DE) wanda aka fara ranar Litinin har sai baba ta gani.
Sanarwa da kakakin hukumar, Dokta Fabian Benjamin, ya fitar ta ce dakatarwar ta fara aiki ne daga ranar Talata, domin fara wasu shirye-shirye da daliban za su yi farin ciki da su.
- Me zai faru bayan rasuwar dan takarar NNPP dab da zabe?
- Tsoffin kudi: Masu kuste sun yi mini lalata —Aisha Buhari
Ya ce da zarar hukumar ta bayyana lokacin ci gaba da rajistar a nan gaba, dalibai masu Shaidar Diploma (OND) ko Takardar Shaidar Koyarwar (NCE) za su dora takardar samun gurbin JAMB ta shafin hukumar, kazalika masu takardar shaidar Sifloma ta jami’a.
A baya dai hukumar ta sanya Litinin a matsayin ranar fara tantance daliban, ta kuma kammala ranar Alhamis.