✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rage kwanakin karatu a makarantun Kaduna ’ya’yan talakawa zai shafa – Iyaye da malamai

Gwamnatin dai ta rage kwanakin karatu zuwa hudu a Jihar.

Iyayen da kuma malaman makarantun gwamnati a Jihar Kaduna sun koka da dokar da Gwamnatin Jihar ta saka na rage kwanakin zuwa makaranta zuwa kwana hudu a mako.

A cewar iyayen da malaman, rage wadannan kwanaki karatun ’ya’yan talakawa zai shafa, wadanda su ne mafi akasari ke zuwa makarantun gwamnati.

A ranar Lahadin da ta gabata ce gwamnatin jihar ta fitar da sanarwa mai dauke da sa hannun Kwamishiniyar Ilimin Jihar, Halima Lawal, inda ta ce an bai wa dukkan makarantun gwamnati da ke jiyar umarnin komawa sabon tsarin na aikin kwana hudu a mako.

A cewar gwamnatin, za ta tabbatar wannan mataki bai shafi tsarin jadawalin karatun daliban ba.

Idan ba a mance ba, a watan Nuwamban bara ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar da sanarwar rage kwanakin aikin gwamnati zuwa kwana hudu a mako maimakon biyar.

Malam Aliyu Suleiman Zaria mazaunin Rigasa ya ce matakin wata alama ce da ke nuna kamar gwamnati ba ta damu da halin da karatun ’ya’yan talakawa zai shiga ba.

“Idan ka dubi abin da ya faru a shekarar 2020 lokacin cutar Kwarona, an rufe duk makarantu, wanda hakan ya yi matukar illa ga karatu. Yanzu bayan an bude makarantu suna kokarin cim ma abin da ya wuce na darussa an kuma fito da wannan tsarin na rage kwanakin karatu.

“Idan yaro bai je makaranta ranar Juma’a ba, me ake so ya yi a gida tun da iyayensa ba su da halin saukar malami da zai koya masa karatu a gida.”

Shi ma Suwidi Zakari Bakanike wanda ’ya’yansa ke zuwa makarantar gwamnati cewa ya yi, “Ni na san ba su damu da karatun ’ya’yan talakawa ba ne, shi ya sa kawai suka kawo wannan sabon salo wai yara su zauna a gida ranar Juma’a. Gaskiya a ra’ayina bai dace ba,” inji shi.

Wani malamin firemare a garin Soba ya bayyana cewa, “kamata ya yi gwamnati ta auna burin da take son cimmawa da wannan mataki a kokarinta na inganta ilimi. Idan muka duba abubuwa da yawa sun faru a fannin ilmin jihar, inda gwamnati ta nuna tana san maido da martabar ilmi da malamai, amma baki daya abin ya zamanto a yanzu babu mutanen da suka fi tozarta a jihar da suka wuce malamai.”

Shi ma wani Malamin firamare a jihar da bai so a ambanci sunansa ya ce, “babu malamin da zai so a ce masa an rage kwana daya domin za ka yi amfani da shi ne wajen tsara darussan da za ka koyawa yara a aji. Idan yana son taimaka wa malaman firamare, wadanda su ne tushen ilimi ko kashin bayan karatun yaro sai ya tabbatar da malaman suna samun hakkinsu akan lokaci na albashi.”