Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce a halin yanzu ragamar mulkin kasar ta koma hannun mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo.
Shugaban ya fadi hakan jim kadan gabanin tafiyarsa a ranar Lahadi zuwa birnin Landan domin duba lafiyarsa.
- Masu garkuwa da mutane 4 sun fada komar ’yan sanda a Gombe
- Romania za ta karbi daliban Najeriya daga Ukraine su karasa karatunsu
Fadar Shugaban Kasar ta sanar cewa Buharin zai dawo gida Najeriya nan da makonni biyu.
Tun a ranar 1 ga watan Maris Hadimin Shugaban Kasa kan Yada Labarai, Femi Adesina Buhari zai je ganin likita a Landan bayan ya kammala halartar taro a Kenya, amma sai ya koma Abuja daga Nairobi.
Mutane da dama dai sun bayyana mamakinsu kan yadda Shugaban ya dawo Abuja daga kasar Kenya, a maimakon birnin Landan kamar yadda aka sanar da farko.
Buharin dai ya halarci wani taro ne a birnin Nairobi na kasar Kenya kan cika shekara 50 da kafa Shirin Muhalli na Majalisar Dinkin Duniya (UNEP), inda daga can ne aka tsara zai wuce Landan din don ganin likitocinsa.
A ranar Juma’a da ta gabata ce Fadar Shugaban Kasar ta tabbatar da cewa Buharin ya dawo Abuja.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai gabanin balaguronsa na ranar Lahadi a filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, shugaba Buhari ya ce Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ne zai ci gaba da riko da akalar jagorancin kasar kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanadar a duk sa’ilin da shi ba ya kasar.
Shugaba Buhari kasancewar ba shi a kasar ba zai hana gwamnati sauke duk wasu nauye-nauye da suka rataya a wuyanta ba, kari a kan cewa yana sane da duk wasu abubuwa da ke gudana ko da ba ya nan.
Da aka tambaye shi kan yadda gwamnati za ta ci gaba da gudanar da harkokinta idan tafi Landan, Buhari ya ce, “ba zan yi ikirarin cewa ni kadai nake tafiyar da harkokin gwamnati ba don a kowane mataki akwai wakilci mai inganci.
“Mataimakin Shugaban Kasa yana nan wanda Kundin Tsarin Mulki ya rataya masa nauyin riko da akalar jagoranci idan ba na nan.
“Sannan kuma muna da Sakataren Gwamnatin Tarayya ga kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Kasa, saboda haka wannan ba wata matsala ba ce,” a cewar Buhari.