Fitaccen malamin addinin Kiristan nan na darikar Katolika, Rabaran Fada Ejike Mbaka, ya ce Peter Obi ba zai taba zama Shugaban Najeriya ba saboda marowaci ne.
Mbaka ya bayyana hakan ne yayin da yake huduba a cocinsa da ke Enugu ranar Laraba, inda ya ce Peter Obi ba shi da kashin kyauta, kuma sanin kowa ne mai hannun jarirai ba ya mulkin Najeriya.
- Zan sake tsayawa takarar Shugaban Kasa a nan gaba – Yahaya Bello
- Takarar Musulmi 2 a APC: Bai kamata APC ta yi watsi da al’ada ba – Lalong
Peter Obi dai shi ne dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023 mai zuwa.
Ya kuma ce gara tsoho mai kyauta ya zamo Shugaban Kasa sau dubu da matashi marowaci.
Rabaran Mbaka, har wa yau ya ce Atiku Abubakar dan takarar PDP ya nuna wa duniya ya gama shirin jagorantar kasar nan, saboda tuni ya yi hannun riga da Peter Obin.
Peter Obi wanda tsohon Gwamnan Jihar Anambra ne zai fafata da dan takarar PDP, Atiku Abubakar da na APC Bola Ahmed Tinubu da kuma Rabi’u Musa Kwankwaso na NNPP.
Rabaran Mbaka ya kuma ce Peter Obi bai ba wa addininsa muhimmanci ba, domin shi ne ya tallafa masa ya samu nasarar sake darewa kujerar Gwamnan Jihar Anambra a karo na biyu, sai dai bai je yayi godiya ga Allah ba bayan hakan ta faru.
“Idan ya zama Shugaban Kasa zai rufe mana gurin ibada ne. Idan al’ummar Ibo na neman wanda zai wakilcesu tun wuri su nemi wani ba Peter Obi ba, mutumin da ba ya ba coci gudummawar komai! Mutumin da ya ci amanar al’ummarsa ya fice daga jam’iyar APGA ya koma PDP, daga nan ya sake ficewa ya dawo LP,” inji Mbaka.
Idan dai za a iya tunawa ko a zaben shekara ta 2019 ma, Mbaka ya yi makamancin wannan hasashen na faduwa zabe ga Peter Obi da Atiku Abubakar, bisa kin ba da gudunmawa ga aikin da cocinsa ke yi a wancan lokacin da Peter din ya yi.