Tun bayan da gwamnatin tarayya ta sanar da aniyarta na dage karin kudin wutar lantarki daga farkon watan Yuli zuwa badi, jama’a da dama ke ci gaba da bayyana mabambantan ra’ayoyi.
Kwatsam sai ga shi bayan wata tattaunawa tsakanin majalisar dokoki ta kasa da Hukumar Dake Kula da Hasken Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) da kuma kamfanonin rarraba wutar sun amince a dage lokacin aiwatar da karin kudin daga daya ga Yulin da aka tsara tun da farko zuwa farkon badi.
Shugabancin majalisar dai ya kalubalanci NERC da kamfanonin kan rashin zurfafa tunani kan irin mummunan tasirin da karin farashin lantarkin zai yi wa ‘yan Najeriya, musamman a halin matsin da suke ciki a yanzu.
- Majalisa ta dakatar da karin farashin wutar lantarki
- Lawan ya caccaki gwamnati kan cefanar da harkar lantarki
Aminiya ta tattauna da wasu magidanta don jin ra’ayinsu kan wannan batu.
Yahaya Abdullahi, mazaunin unguwar Kofar Famfo a Kano ya shaida wa Aminiya cewa yana amfani da mita mai kati ne a gidansa, ko da yake ya koka kan cewa yanzu ba su cika samun wutar kamar kwanakin baya ba.
Idan ana bayar da wuta za mu biya
“Gaskiya yanayin samuwar wutar yanzu da sauki, ba kamar kwanakin baya ba, farkon saka dokar kulle, ko da yake lokacin ma an ce mana sakamakon kamfanoni da ba su aiki ne ya sa muke shan wutar”, inji Abdullahi.
Ya kara da cewa, “A zahirin gaskiya mu babbar matsalarmu ita ce samun wadatacciyar wutar ba tare da daukewa ba. Ko nawa ne in dai za a samu za mu ci gaba da biya.
“Amma abun da ba za mu lamunta ba shi ne karin kudin wutar ba tare da an inganta ta ba. A matsayina na mai amfani da mita ba ni da matsalar biyan kudi, yawanci ma kafin kati ya kare nake sayen sabo”, a ta bakinsa.
A bar maganar karin kudin wuta
To sai dai ba duka aka taru aka zama daya ba, domin kuwa Malam Adamu Sabo mazaunin unguwar Adakawa a Kanon ya ce ba da mita mai kati yake amfani a gidansa ba, ko da yake ba ma kullum suke samun wutar ba.
Ya ce, “Ni kiran ma da zan yi shi ne gwamnati da wadannan kamfanonin su dubi Allah su dubi Ma’aiki su jingine batun karin kudin wutar nan, la’akari da halin da ake ciki kowa ta kansa yake yi”.
Da Aminiya ta tambaye shi kan nawa yake biyan kudin wutar, ya ce ya kan biya Naira 1,500 ne a duk wata.
A nasu bangaren kuwa, kamfanonin raba wutar lantarki sun ce duk da dai suna so a aiwatar da karin kamar yadda aka tsara tun da farko, amma za su hakura su jira har zuwa badin.
Ba aljihunmu kudin za su shiga ba
A tattaunawarsa da Aminiya, Kakakin Kamfanin Rarraba Hasken Wutar na Kano (KEDCO), Ibrahim Sani Shawai ya ce a matsayinsu na kamfanonin rarraba wutar, ba su da matsala da canza shawarar kan karin kamar yadda aka tsara tun da farko.
Ya ce, “Abun da muke so mutane su fahimta shi ne hanyoyin da ake bi tun daga samar da wutar zuwa dakonta da kuma rarraba ta sun kara tsada matuka.
“Abun da yake faruwa a kullum shi ne idan Naira shida ake samar da wutar alal misali, to su masu amfani da wutar abun da suke biya bai wuce Naira uku ba a ciki, ita kuma gwamnati ta cikasa ragowar Naira ukun.
“Hakan ya sa gwamnati take narkar da makudan kudade wajen cike gurbin abun da mutane suke gaza biya a duk wata, ka ga ke nan wannan ba mai yiwuwa ba ne gwamnati ta ci gaba da yin hakan.
“Wannan dalilin ne ya sa gwamnatin ta yanke shawarar kara kudaden wuta, ba wai aljihun kamfanonin rarraba wutar lantarkin za su koma ba”, inji Shawai.
Mutane da ba sa biyan kudin wuta
Kakakin na KEDCO ya kuma lura cewa da dama daga cikin abokan huldarsu ba da mita suke amfani ba, ko da yake ya ce tuni kamfanin nasu ya yi nisa wajen ganin ya samar da mita ga kowane gida.
Kazalika, Shawai ya koka matuka kan cewa akasarin mutane ba sa iya biyan kudaden wutar da su ke sha a karshen wata kamar yadda ya kamata.
Gwamnatoci da yawa a Najeriya dai sun dade suna kokarin shawo kan matsalar samar da isashshiyar wutar lantarki, ko da yake ya zuwa yanzu matsalar ta ki ci ta ki cinyewa.