Wannan hoto hadi ne – Abubakar Ibrahim
A tunanina wannan bidiyon yarfe ne na ’yan siyasa. A tarihin siyasa an saba yi wa shugabanni yarfe, domin ina iya tunawa an ce Abubakar Rimi dan tatsine ne, an ce Kwankwaso ya zagi Annabi (SAW) an ce Shekarau ya yi wa mace ciki kafin ya aure ta. Don haka wannan ba sabon abu ba ne. Na biyu kuma ni ban ma yarda da sahihancin hoton bidiyon ba domin duk mai hankali idan ya kalli hoton da kyau zai gano cewa hadi ne, saboda hotunan an dauke su a shekara daban-daban amma idan aka duba riga guda daya ce a jikin Gwamnan. Kuma hannu daya ne ya bayar da kudin a dukan hotunan. Idan gaskiya ne to ina mai ba shi kudin, don haka gaskiya akwai lauje cikin nadi.
Wannan aikin kwamfuta ne kawai – Sani Yakubu
Abin da zan ce kallon kura iyawa ne domin akwai abin da idan ka gani za ka gane gaskiya ne. Kuma idan ka duba Allah Ya kawo mu zamani za a iya daukar hoto a hada a kwamfuta.
An yi haka ne don a bata wa Gwamnan suna -Nurudden ABDK
Ina ganin an fitar da hoton ne don kawai a ci mutuncin Gwamna, domin a wannan zamani babu abin da ba za a iya yi da na’urar kwamfuta.
Ganduje ba zai aikta cin hanci da rashawa ba – Anas Aliyu Danja
Ni ban da ma batun hadin hoto da nake tunanin an yi don a bata sunan Gwamnan. Ba na tunanin za a iya samun Mai girma Gwamna da cin hanci da rashawa saboda shi shugaba ne adali haka kuma shugaba ne na kwarai. Wannan abu kage ne da ake tunanin wani bangare na ’yan adawa suka kulla wa Gwamnan don su ga sun tadiye shi don kaiwa ga smaun nasara a zabe mai zuwa. Kasancewar sun hango nasara a tattare da Gwamnan.
Allah Ya bayyana gaskiya – Sadiku Kabiru
Abin da zan ce shi ne Alllah Ya bayyana gaskiya a cikin lamarin, wato idan har Ganduje ya aikata wannan abu na cin hanci Allah Ya nuna gaskiyar lamarin idan kuma bai aikata ba Allah Ya wanke shi.
Abin ya ba mu mamaki – Abdussalam Abubakar
Gaskiya mun shiga cikin dimuwa da mamaki yadda za a samu mai dokar barci ya buge da gyangyadi. Mutanen da za a ce su ne masu hanawa amma kuma a same su suna aikatawa. Wannan lamari abin kaico ne ga duk al’ummar Jihar Kano.