✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Qatar: Me kuka sani game da kasar da za ta karbi bakuncin Gasar Kofin Duniya ta 2022?

Ko kun san salsalar arzikin Qatar?

A ranar 21 ga watan Nuwamban da muke ciki ne za a soma Babbar Gasar Tamaula ta Duniya wato Gasar Kofin Duniya ta 2022.

Ku ci gaba da kasancewa da shafukanmu na Aminiya domin samun rahotanni kai tsaye gabanin soma gasar da kuma yayin da take wakana har ma da bayanta, inda za mu watso muku sharhi da fashin baki dangane da ababen da za su wakana.

Kafin nan dai za mu soma ne da kasar da za ta karbi bakuncin wannan babbar gasar ta bana, wato kasar Qatar.

Wacce kasa ce Qatar?

Qatar kasa ce a Yammacin nahiyyar Asiya wadda take makwabtaka da alkaryar Larabawa a Arewa maso Gabashi sannan kuma ta yi iyaka da kasar Saudiyya a Kudanci yayin da Tekun Fasha ya mamaye sauran yankinta.

Haka kuma, Tekun Bahrain wanda dan tsakure ne na Tekun Fasha, shi ne ya yi wa Qatar iyaka da makwabciyarta Bahrain. Babban birnin Qatar dai shi ne Doha, wanda ya kasance matsugunnin kashi 80 cikin 100 na adadin al’ummar kasar.

A halin yanzu dai Qatar ita ce kasa ta uku mafi girman tattalin arziki a duk kasashen Larabawa. Ita ce kasa ta uku mafi arzikin man fetur a duniya mai tarin rijiyoyin mai.

A yanzu haka dai Qatar na daya daga cikin kasashen da ke sahun gaba-gaba wajen fitar da iskar gasa a duniya.

Salsalar arzikin Qatar 

A cikin karni na 21 ne Qatar ta shiga sahun kasashe mafi karfi a Gabas ta Tsakiya saboda tarin albarkatunta, ta kuma shahara musamman ta hanyar Kafar Watsa Labarai ta Al Jazeera da samar, inda sunan kasar ya yadu kusan ko’ina a doron kasa.

A wancin lokacin, an rika zargin Qatar da goyon bayan ’yan tawaye masu adawa da tsare-tsaren gwamnati a yankin na Larabawa, inda ake kallonta a matsayin kasar da ke tallafa wa ’yan tawayen da guminta.

Qatar ta samu damar kasancewa mai karbar bakuncin Gasar Kofin Duniya ta 2022 a cikin wani yanayi mai cike da cece-kuce, wanda hakan ya sa ta kasance kasar Musulmi ta farko a kasashen Larabawa da za ta karbi bakuncin gasar.

Kamar yadda tarihi ya nuna, Qatar ce ta karbi bakuncin wasannin Asiya a 2006, kuma ita za ta karbi bakuncin wasannin Asiya a shekarar 2030.

Bambancin gasar ta bana da na shekarun baya

Gasar Kofin Duniya ta bana da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ita ce babbar gasar ajin maza ta 22 da za ta gudana a tarihi kuma ake gudanar da ita duk bayan shekara hudu a tsakanin tawagar Kwallon Kafa ta kasashe mambobin FIFA.

Kuma kamar dai yadda aka sani, gasar za a soma gasar ce daga ranar 21 ga Nuwamba zuwa 18 ga watan Disamba na wannan shekara da muke ciki a Qatar.

Za ta kasance Gasar Kofin Duniya ta farko da za a buga a kasar Larabawa kuma ta biyu a tarihi da za a buga a nahiyar Asiya bayan wadda aka buga a Koriya ta Kudu da Japan a shekarar 2002.

Kuma kamar dai yadda aka saba, za a buga gasar a tsakanin tawagar kasashe 32, sai dai wannan shi ne karo na karshe da za a ci gaba tafiya a kan wannan tsari.

Mahukunta sun tabbatar cewa za a kara yawan gurbin kasashen da za su rika fafata babbar gasar zuwa 48, kamar dai yadda za a gani a Gasar Kofin Duniya ta 2026 da za a buga a kasashen Amurka, Mexico da kuma Canada.

Saboda tsananin zafi da kasar Qatar ke fama da shi, wannan gasar za ta gudana ne daga karshe-karshen watan Nuwamba zuwa tsakiyar watan Disamba, lamarin da zai sa ta zama gasar ta farko da ta sha bam–ban da lokutan da aka saba bugawa na watan Mayu, Yuni ko Yuli ba.

A bana dai, za a buga gasar ce a lokacin kaka, inda za a buga ta a cikin dan gajeren lokaci na kusan kwanaki 29.

Wasan farko da za a fafata zai kasance tsakanin mai masaukin baki Qatar da Ecuador a filin wasa na Al Bayt a Al Khor.

Haka kuma, wasan karshe zai gudana a ranar 18 ga Disamba, 2022, wanda kuma ita ce Ranar Kasa ta Qatar.

Shirin da Qatar ta yi 

Qatar mai yawan al’umma miliyan 2.9 na daya daga cikin kasashe mafiya arziki a duniya saboda arzikin man fetur da gas da take da su.

Ta gina sabbin filayen wasa bakwai kawai saboda gasar, da kuma wani sabon birni da za a buga wasan karshe a cikinsa.

Ana gina sabbin otel sama da 100, da sabuwar tashar jirgin kasa da wasu tituna.

Kwamitin shirya gasar ya yi kiyasin cewa ana sa ran mutum miliyan daya da rabi ne za su halarce ta.

Qatar kasar Musulmi ce mai bin addini sau da kafa. An gargadi magoya baya da su kasance masu da’a.

Akwai dokokin hana shan giya. Ana iya saya ne a manyan otel-otel kawai. Kofi daya na giya kan kai dala 13 – kwatankwacin naira 5,000.

Sai dai masu shirya gasar sun ce za a iya sayar da giyar a wasu kebantattun wurare na ‘yan kallon gasar.

Takarar karbar bakuncin 

A 2010 ne Qatar ta yi nasarar samun damar karbar bakuncin gasar ta hanyar lashe zaben da Fifa ta shirya tsakanin mambobinta 22. Ta doke kasashen Amurka da Japan da Australia.

An zargi Qatar da bai wa jami’an tsaro cin hancin dala miliyan uku da dubu 700 don samun damar, amma an wanke ta bayan kwashe shekaru biyu ana gudanar da bincike.

Shugaban FIFA na lokacin, Sepp Blatter, ya goyi bayan bukatar Qatar a lokacin amma ya ce da alama FIFA ta yi kuskure.

Yanzu haka an wanke Mista Blatter bayan fuskantar shari’a a kotu a Switzerland bisa zargin zamba da almubazzaranci da sauran tuhumar cin hanci da rashawa.

Kazalika, kungiyoyin kare hakki na Amnesty International da Human Rights Watch na zargin Qatar da take hakkin ma’aikata ’yan kasar waje suka yi aikin gina filayen wasannin gasar.

Kasashe 32 da za su fafata a Qatar

Kasashen sun hada da Argentina, Brazil, Ingila, Faransa, Sifaniya da Belgium.

Akwai Portugal, Jamus, Netherlands, Uruguay, Croatia, Denmark, Mexico da kuma kasar Amurka.

Sauran su ne, kasar Senegal, da Wales, Poland, da Austaraliya, Japan, Morocco, Switzerland, Ghana da kuma Koriya ta Kudu.

Sai kasar Kamaru, Sabiya, Canada, Costa Rica, Tunisiya, Saudi Arabia, Iran, da Kasar Ecaudor da masu masaukin baki kasar Qatar.

Yadda aka raba rukunin kasashen da za su fafata 

Rukuni na farko: Qatar, Ecuador, Senegal, Netherlands

Rukuni na biyu: Ingila, Iran, Amurka, Wales

Rukuni na uku: Argentina, Saudiyya, Mexico, Poland

Rukuni na hudu: Faransa, Australia, Denmark, Tunisia

Rukuni na biyar: Spain, Costa Rica, Jamus, Japan

Rukuni na shida: Belgium, Canada, Morocco, Croatia

Rukuni na bakwai: Brazil, Serbia, Switzerland, Kamaru

Rukuni na takwas: Portugal, Ghana, Uruguay, Koriya ta Kudu

%d bloggers like this: