✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Qatar 2022: Zargin tauye hakkokin baki ya dabaibaye Qatar

Kwana 20 kafin fara Gasar Kofin Duniya na 2022 a Qatar, an samu karuwar korafe-korafare ka biyan hakkokin ’yan kasashen waje da ke aiki a…

Kwana 20 kafin fara Gasar Kofin Duniya na 2022 a Qatar, an samu karuwar korafe-korafare ka biyan hakkokin ’yan kasashen waje da ke aiki a kasar.

A ranar 20 ga watan Nuwamba da muke ciki za a fara gasar a kasar Qatar, wadda ta yi kaurin suna wajen musguna wa ma’akata ’yan kasashen waje da tauye hakkin mata.

Hukumar Kwadago ta Duniya (ILO) ta ce ’yan kasar waje da ke aiki a Qatar sun shigar da korafe-korafe 34,425 ta intanet cewa iyayen gidansu a kasar na kin biyan su hakkokinsu.

“Ma’aikatan sun fi yin korafi a kan kin biyan su albashi, rashin biyan su hakkokinsu na sallama da kuma kin ba su hutun shekara-shekara kuma ba a biyan su alawun din rashin hutu,” in ji Hukumar.

Sanarawar da hukumar ILO ta fitar a ranar Talata, ta kara da cewa, an kai sama da 10,500 daga cikin korafe-korafen gaban kotu, kuma kusan daukacin alkalan sun ba wa ma’aikatan gaskiya.

Qatar dai ta yi kaurin suna wajen tauye hakkokin baki ma’aikata, matsalar da Majalisar Dinkin Duniya ta ce wajibi ne kasar ta yi gyare-gyare kan dokokinta domin kawo karshenta.

Sai dai rahoton ILO ya bayyana cewa an samu raguwar ma’aikatan da suka gamu da matsala saboda tsananin yanayin zafin Qasar sakamakon sabbin dokokin da hukumomin kasar suka kafa a 2021.

Kungiyar agaji ta Red Crescent da ke kasar ta ce cibiyoyin lafiyarta sun kula da irin wadannan ma’aikata 351 a bana, sabanin 620 da ka samu a 2021, da kuma 1,320 a 2019.

Sai dai ILO ta ce duk da haka, “akwai bukatari karin sauye sauye domin inganta dokokin kwadaga a kasar Qatar.