✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Qatar 2022: Saudiyya ta lallasa Argentina a Gasar Cin Kofin Duniya

Sakamakon wasan dai ya zo da ba-zata

A ci gaba da fafata wasanni a Gasar Cin Kofin Duniya da take gudana a kasar Qatar, Saudiyya ta lallasa Argentina, kasar da Lionel Messi yake buga wa wasa da ci biyu da daya.

Wannan nasarar dai ta zo wa jama’a da ba-zata, kuma tana daya daga cikin abubuwan da suka fi daure kai a tarihin gasar.

Messi ne dai ya fara zura wa Argentina kwallo ta farko, kafin daga bisani Saudiyya ta farke kwallo biyu cikin mintuna biyar bayan dawowa hutun rabin lokaci.

Sai dai a yayin wasan, alkalin wasan ya soke kwallayen da Messi da Lautaro Martinez suka ci, bayan na’urar VAR ta nuna sun yi satar gida.

A haka dai mai tsaron ragar Saudiyya ya ci gaba da tare dukkan hare-haren da aka rika kai musu, har aka busa tashin karshe.

Yanzu dai Argentina za ta fafata wasanta na gaba da kasar Mexico a rukunin C ranar Asabar mai zuwa.