✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Qatar 2022: Kocin Brazil ya ajiye aikinsa

Bayan rashin nasara a hannun Crotia, Tite wanda ya jagoranci Brazil wajen lashe Gasar Copa America a 2019 ya yi murabus

Kocin Brazil, Tite, ya ajiye aikinsa na horar da tawagar ’yan wasan kasar bayan rashin zuwa matakin Kusa Da Na Karshe a Gasar Kofin Duniya da ke gudana a kasar Qatar.

Tite ya ajiye aikinsa ne jim kadan bayan Crotia ta doke Brazil a bugun fanareti a wasan Kwata-Fainal da suka buga ranar Juma’a.

A matakin Kwata-Fainal, Croatia ta fitar da Japan a zagayen ’Yan 16 a bugun fanareti, sannan ta maimaita irin wannan nasara a karawarta da Brazil a yammacin ranar Juma’a.

A 2016 ne Tite ya karbi ragamar horar da tawagar ’yan wasan, inda ya jagorance ta wajen lashe Gasar Copa America a 2019.