Shugaba Bola Tinubu ya magantu kan halin ƙuncin rayuwa da ya addabi al’ummar Najeriya yana mai tabbatar da cewa lallai ana fama da yunwa a ƙasar.
Sai dai shugaban ya ba da tabbacin cewa sauƙi na tafe nan gaba kaɗan saboda wasu tsare-tsare da yake ɗauka domin kawo ƙarshen matsalolin.
- Kashi 63 na ’yan Najeriya ba su samun wadataccen abinci saboda talauci — NBS
- ’Yan bindiga sun sace mutum 12 a Kaduna
Wata sanarwa da hadiminsa a ɓangaren sadarwa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Tinubu ya bayyana hakan ne yayin ƙulla yarjejeniyar inganta harkokin sarrafa naman dabbobi da wani kamfani a birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil.
Tinubu ya ce akwai wasu muhimman tsare-tsare da gwamnatinsa ta shimfiɗa domin kawo bunƙasa harkokin noma da kiwo.
Shugaban ya kuma faɗi yadda yake ƙoƙarin shawo kan matsalolin ƙarancin abinci da kuma rigimar manoma da makiyaya. Tinubu ya tabbatar akwai yunwa a Najeriya
“Muna ƙoƙarin magance ƙuncin rayuwa da ake fama da rashin tabbas ta hanyar inganta tattalin arziki.
“Za mu yi duba zuwa matsalolin da muke da su a ƙasar domin kawo damarmaki da ke ciki.
“Samar da abinci yana da matuƙar muhimmanci, amma a yanzu da muke magana akwai yunwa sai dai akwai haske a gaba wanda kowa zai shaida hakan.”