Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ke kasar Spain ta kafa tarihin zama kungiyar da ta fi yawan ’yan wasan da ke buga kofin duniya a gasar da yanzu haka ake gudanarwa a Qatar.
Yanzu haka dai kungiyar na da ’yan wasanta har guda 17, adadin da ya haura guda 15 din da suka buga wasa daga kungiyar ga kasar Brazil a shekarar 2014.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Bauchi Da Gombe Ke Kallon Hakar Mai A Yankinsu
- Yau ake fara hako danyen mai a Arewacin Najeriya
Kungiyar Bayern Munich da Manchester City ne suke biye wa Barcelona baya da yawan ’yan wasa 16, kowaccensu.
A mataki na uku kuwa, kungiyar Al-Sadd da ke kasar Qatar ce da ‘yan wasa 15, sai Manchester United ta Ingila mai ’yan wasa 14 da ke buga gasar a yanzu haka.
Su kuwa kungiyoyin Real Madrid da Chelsea da Athletico Madrid da kuma Al-Hilal ta kasar Saudiyya, dukkansu na da ’yan wasa 12 da ke buga wa kasashe daban-daban gasar.
An dai fara gudanar da gasar ta bana ce a kasar Qatar ranar Lahadi, karon farko a tarihi da wata kasar Larabawa ta karbi bakuncin shirya gasar.