✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan Farko A Gasar Kofin Duniya

Gasar Cin Kofin Duniya ta shekarar 1930 ita ce ta farko a tarihin duniyar kwallon kafa.

A ranar Lahadi, 20 ga Nuwamba, 2022 aka fara Gasar Kwallon Kafa ta Cin Kofin Duniya na 2022 kasar Qatar.

Ga jerin wasu muhimman abubuwa da lokutan da aka fara yin su a tarihin gasar:

Kofin Duniya na Farko

Gasar Cin Kofin Duniya ta shekarar 1930 ita ce ta farko a tarihin duniyar kwallon kafa.

Masu masaukin baki na farko

An fafata gasar Kofin Duniya ta farko ce a kasar Uruguay tsakanin 13 zuwa 30 na watan Yulin shekarar 1930.

Fara zuwa kwallo

Wanda ya fara cin kwallo a Gasar Kofin Duniya shi ne Lucien Laurent na kasar Faransa a minti 19 da fara wasa a gasar Kofin Duniya ta farko.

Farkon lashe gasar

Kasar Uruguay ce ta lashe gasar ta farko a wasan karshe da aka buga a ranar 30 ga watan Yulin 1930, inda ta doke Ajantina da ci hudu da biyu a gaban ’yan kallo 93,000.

Mafi zura kwallaye

Dan wasan kasar Ajantina Guillermo Stabile, wanda daga baya ya zama koci, shi ne mutum na farko da ya fi zura a gasar ta farko.

Farkon jan kati

Dan wasan kasar Peru, Placido Galindo shi ne dan wasan farko da aka ba wa jan kati a Gasar Cin Kofin Duniya a wasan kasarsa da Romania, wanda rafare Alberto Warnken ya yi alkalanci.

Fanaretin farko

Farkon fanareti da aka buga a Gasar Cin Kofin Duniya shi ne wanda dan kasar Chile Carlos Vidal ya buga a ranar 19 ga Yulin 1930 a wasansu da kasar Faransa.

Farkon kama fanareti

Golan Faransa, Alexis Thepot ne ya fara kama fanareti a Gasar Cin Kofin Duniya a wasansu da kasar Chile.

Cin fanareti

Wanda ya fara cin fanareti a Gasar Cin Kofin Duniya shi ne dan wasan Mexico Manuel Rosas a wasansu da Ajantina a ranar 19 ga Yulin 1930.

Cin kwallo uku rigis

Dan wasan da ya fara cin kwallo uku rigis wato hat trick a gasar cin shi ne Bert Patenaude na kasar Amurka a wasansu da Paraguay a 1930.

Canjin dan wasa

Dan wasan da aka fara canjawa a Gasar Kofin Duniya shi ne golan Faransa Alex Thepot wanda ya samu rauni a wasan farko na gasar ta farko, inda Augutin Chantrel ya canje shi.

Rafaren farko

Rafaren da ya busa wasan farko na Gasar Kofin Duniya shi ne John Langenus dan kasar Belgium.