✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Putin ya yi ta’aziyyar mutuwar Shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin

Putin ya ce Prighozin dan kasuwa ne mai basira.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya jajanta kan mutuwar shugaban kamfanin sojojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin, wanda tsohon mai dafa masa abinci ne.

A wani jawabi da ya gabatar a talabijin, Putin ya ce kamfanin Wagner ya ba da gagarumar gudunmawa ga Rasha a Ukraine.

Putin ya kara da cewa Rasha za ta yi bincike kan lamarin da ya jawo hatsarin jirgin da a cikinsa Prigozhin ya rasa ransa, tare da mutum tara a Rasha a ranar Laraba.

Putin ya mika sakon ta’azziyarsa ga iyalan mutanen da suka mutu a hatsarin da ya faru a yankin Tver, mai nisan kilomita 200 daga birnin Moscow a Arewa maso Yamma.

A cewar Putin, Prighozin “dan kasuwa ne mai basira, wanda ya san shi tun shekarun 1990.”

Putin ya ci gaba da cewa Prigozhin mutum ne da ya dinga “haduwa da kaddarar rayuwa wanda kuma ya aikata kura-kurai a rayuwarsa.”