Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin, ya ce ba da wasa yake ba kan barazanar da ya yi ta amfani da makaman kare-dangi kan kasashen Yamma don ya kare kasarsa.
A karo farko tun bayan kammala Yakin Duniya na Biyu, Putin a ranar Laraba ya umarci masu kula da tashar a kasar shi da su kasance cikin shiri, sannan ya ware karin sojoji 30,000 da suke shirin ko-ta-kwana.
- ASUU za ta daukaka kara kan umarnin kotu na komawa bakin aiki
- Ummita: Majalisa ta bukaci a binciki zargin kisan da dan China ya yi a Kano
Tun bayan mamayar da kasarsa ta yi wa Ukraine a watan Fabrairun da ya gabata, Putin ya kara nuna yiwuwar amfani da makaman na Nukiliya bayan ya kwace iko da sassa da dama na Ukraine din da fadinsu ya kai kwatankwacin girman kasar Hungary.
A wani jawabinsa ga al’ummar kasar da aka watsa ta gidan talabijin, Shugaba Putin ya ce, “Matukar aka yi barazana ga ’yanci da matsayin kasarmu, to kuwa babu shakka za mu yi amfani da kowanne ikon da muke da shi wajen kare Rasha da mutanenta.”
Shugaban, wanda ya fake da ci gaba da mamayar da kungiyar kawancen tsaro ta NATO ke yi, ya ce kasashen Yamma, musamman Amurka, Tarayyar Turai da Birtaniya na kokarin yin amfani da makaman a kan kasarsa, tare da ziga Ukraine ta mayar da martani har a cikin Rasha.
Putin ya ce, “Wannan kokarin tsokanar fada ne, kasashen Yamma sun yi duk wani abu don su takale mu.
“Ba wai cika baki nake ba, kuma ba da wasa nake ba, amma muddin suka kuskura suka yi amfani da makaman Nukliliya a kan mu, to babu shakka za su dandana kudarsu,” inji Putin.