Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin ya kori ma’aikatansa akalla 1,000, saboda fargabar da yake yi kan za a iya amfani da su wajen saka masa guba a abinci.
Wasu bayanai daga Fadar Gwamnatin Kasar da ke Kremlin sun tsegunta cewa Shugaban ya dauki matakin ne a watan Fabrairun da ya gabata.
- An daddatsa fasto a Kogi, an jefa gawarsa a kwata
- An daura auren jikar Ado Bayero da basaraken Yarabawa a Kano
Rahotanni sun ce ya kori ma’aikatan ne wadanda suke da alaka da abincinsa da sauran hadimansa su 1,000 saboda gudun kada a yi amfani da su wajen cutar da shi.
Galibi dai Putin na da ma’aikatan da ke fara dandana duk abincin da aka kawo masa, kafin ya fara ci.
Daga cikin ma’aikatan da aka kora har da dogaransa da masu daga masa abinci da masu yi masa wanki ga guga da kuma sakatarorinsa.
Amfani da guba dai wajen kashe ‘yan siyasa ba sabon abu ba ne a Rasha.
Ko a shekarar 2020 dai sai da aka kashe jagoran ’yan adawar kasar, Alexei Navalny, ta hanyar amfani da guba, inda ake zargin Shugaba Putin din da hannu a ciki.