✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PSG za ta raba gari da Ramos, Tottenham za ta dauki Conte

PSG na shirin sauya shawararta a kan kwantiragin shekara biyu da ta kulla da Ramos.

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta fara tattaunawa da tsohon manajan Chelsea, Antonio Conte a wani yunkuri na bashi ragamar horar da kungiyar bayan korar manajanta Nuno Espirito a ranar Litinin sakamakon rashin katabus da kungiyar ke ci gaba da yi a wannan kaka. (Goal)

Antonio Conte na shirin sanya hannu a yarjejeniyar fam miliyan 20 a matsayin sabon manajan Tottenham inda ’yan wasan kungiyar ke shirin tsohon kociyan na Chelsea da Inter Milan mai shekara 52, ganin ya jagorance su a atisaye ranar Talatar nan.(Telegraph)

Tuni ma har Conten ya bukaci shugaban Tottenham Daniel Levy ya ware kusan fam miliyan 237 domin sayen wasu ’yan wasan gasar Italiya ta Serie A, su shida da yake son daukowa. (Calciomercato, daga Express)

Antonio Conte

Haka kuma kungiyar ta Tottenham na shirin biyan Nuno Espirito Santo kudin sallama da ya kai fam miliyan 14. Amma kuma da a ce an kai karshen kaka, to yarjejeniyar daukar kociyan dan Portugal ta tanadi sallamarsa ba tare da biyansa komai ba idan ba su kare gasar a cikin shidan farko ba a Premier. (Sun)

Nuno Espirito Santo

Kungiyar Al Sadd ta sanar da Barcelona cewa lalle sai sun je Qatar idan suna son a tattauna da su domin daukar Xavi Hernandez, mai shekara 41, ya zama sabon kociyan kungiyar ta Sifaniya. (AS)

Har ma dai Xavi ya bai wa Barcelona sunayen ’yan wasa hudu da yake son a dauko masa, ciki har da Paul Pogba na Manchester United mai shekara 28, wanda zai kasance ba wata yarjejeniyar wata kungiya a kansa a karshen kaka. (El Nacional)

Xavi Hernandez

Liverpool da Arsenal sun bi sahun Juventus da AC Milan da kuma Borussia Dortmund wajen gabatar da bukatarsu ta daukar Marco Asensio daga Real Madrid a watan Janairu, amma kuma kungiyar Jamus din ce kusan dan wasan na tsakiya dan Sifaniya mai shekara 25 ya fi so. (El Nacional )

AC Milan na shirin sake kara wa dan wasan gabanta dan Sweden Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 40, karin kwantiragi, kamar yadda sharadin na yanzu yake. (Calciomercato)

Newcastle ta shirya bayyana sabon mai horas da ’yan wasanta a wannan makon, inda manajan Villarreal kuma tsohon na Arsenal Unai Emery, mai shekara 49, ke kan gaba a yanzu. (Mirror)

Arsenal na duba yiwuwar dauko dan wasan gaba na Torino da Italiya Andrea Belotti, mai shekara 27. (Calciomercato)

Arsenal na shirin mika bukatar karbar aron dan wasan gaba na Serbia Luka Jovic, mai shekara 23, daga Real Madrid. (Express)

Akwai yiwuwar matsin lamba ya sa Juventus ta sayar da dan wasn tsakiya na Wales Aaron Ramsey, mai shekara 30, ko kuma Weston McKennie, na Amurka mai shekara 23, domin samun kudin sayen dan wasan gaba na Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 21 daga Fiorentina da kuma dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund, dan Belgium Axel Witsel, mai shekara 32. (Tuttosport)

Paris St-Germain ta fara duba yiwuwar sauya shawararta a kan kwantiragin shekara biyu da ta kulla da Sergio Ramos, mai shekara 35, wanda ya koma can bayan zamansa da Real Madrid ya kare watan Yuli, wanda har yanzu bai yi mata wasa ba saboda rauni. (Le Parisien)

Zlatan Ibrahimovic ya ci kwallonsa cikon ta 400 a wasannin Lig-Lig bayan kwallon da ya ci a wasan da AC Milan ta yi nasara a kan Roma da ci 2 -1 a gasar Seria A.

Zlatan Ibrahimovic

Ibrahimovic, mai shekaru 40, ya fara cin kwallon ne a mintia na 25 wadda kuma ita ce cikon ta 150 da ya ci a gasar ta Italiya.