Kungiyar Kwallon Kafa ta PSG ta nada tsohon kocin Spain da Barcelona Luis Enrique a matsayin sabon mai horas da ‘yan wasanta.
Kocin mai shekaru 53 ya maye gurbin Christophe Galtier wanda kungiyar ta kora duk da cewa, ya lashe mata kofin gasar Lig 1 a cikin kaka daya tilo da ya jagoranci kungiyar.
- Take hakkin kananan yara na karuwa a duniya — MDD
- Gwamanan Sokoto ya yi tarar makara a Gidan Gwamnati
Kafofin watsa labaran wasanni sun ruwaito cewa Enrique ya kulla yarjejeniyar shekaru biyu da PSG.
A karon farko ke nan da Enrique ke aikin horaswa tun bayan da ya raba gari da tawagar Spain a cikin watan Disamban bara bayan kasar ta sha kashi a hannun Morocco a bugun fenariti a gasar cin kofin duniya, matakin ‘yan 16.
Ya dai taka rawa a lokacin da yake horas da Barcelona, inda ya lashe mata kofuna tara a kakar wasanni uku tsakanin shekarar 2014 zuwa 2017 da suka hada da kofin gasar zakarun Turai da La Liga da Copa del Rey.