Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta doke Real Madrid da ci daya mai ban haushi a Gasar Zakarun Turai (UEFA Champions League).
Kungiyoyin biyu sun kara ne a mataki na biyu na gasar wanda aka yi a ranar Talata a filin wasa na Pac de Prince, da ke Paris, babban birnin kasar Faransa.
- Yajin aiki: Malaman kwalejojin ilimi na barazanar bin sahun ASUU
- HOTUNA: Yadda karancin mai ya kawo cikas ga harkar sufuri a Abuja
An shafe kashin farko na wasan ba tare da kowace kungiya ta zura kwallo a ragar abokiyar hammayarta ba.
Kazalika, Lionel Messi ya zubar da bugun fanareti da PSG ta samu a minti na 62, bayan kayar da Mbappe da Carvajal ya yi a yadi na 18.
Dan wasan gaban PSG, Kyliam Mbappe ne ya zura kwallo a minti na 93, ana dab da tashi daga wasan.
PSG ta yi bajinta tare da kayatar da ’yan kallonta, inda ta buga kwallo cikin gwaninta.
Nan gaba Real Madrid za ta karbi bakuncin PSG a zagaye na biyu na gasar a ranar 9 ga watan Maris, 2022 don kammala zagaye na biyu na wasan don fidda wanda zai je zagaye na gaba na gasar na UEFA Champions League.