Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta dauko Mauricio Pochettino a matsayin sabon mai horas da ’yan wasanta.
PSG ta nada Pochettino ne bayan sallamar Thomas Tuchel da ta yi a satin da ya gabata.
- Wata mata ta antaya wa kishiyarta tafasasshen ruwa
- Ronaldo ya yi fice a harkar kwallon kafa —Messi
- Messi ya share tarihin da Pele ya kafa a kwallon kafa
- Ronaldo ya jefa kwallaye 750 a tarihinsa na kwallon kafa
Tuchel ya shekara biyu da rabi yana jan ragamar kungiyar ta PSG.
Kafin sallamarsa ya lashe gasar cin kofin Ligue 1 na kasar Faransa har sau biyu, sai gasar Coupe de France and Coupe de la Ligue.
Kafin zaman Pochettino sabon kocin kungiyar, ya horar da kungiyar Tottenham, kafin a sallame shi a watan Nuwamban 2019.
Pochettino, ya horar da kungiyar Espanyol daga 2009 zuwa 2012, daga nan ya karbi ragamar Southampton sannan Tottenham.
Kafin zamansa mai horarwa, ya buga wasa a matsayin dan wasan PSG a shekara ta 2001 zuwa 2003.