✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Portugal ta sallami Fernando Santos daga aikinsa

Portugal ta raba gari da kocin, bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Maroko.

Hukumar kwallon kafa ta Portugal ta sallami kocin tawagar ’yan wasan kasar, Fernando Santos daga aikinsa.

Wannan na zuwa ne kwana uku bayan rashin nasara da Portugal ta yi da ci daya mai ban haushi a hannun Maroko a matakin Kwata-Fainal a Gasar Kofin Duniya da ake yi a Qatar.

Santos dai ya ajiye Ronaldo a wasan da Portugal ta yi da Switzerland, wanda ta yi nasarar jefa kwallo 6 da daya a raga.

Amma wasan da Maroko ta yi waje da Portugal ya bar baya da kura, musamman yadda kocin ya sake ajiye Ronaldo a benci har sai bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Santos ya jagoranci Portugal wajen lashe Gasar Europe a 2016 da kuma kofin ‘UEFA Nation League’ a 2019.

Hukumar kwallon kafa ta kasar, cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Alhamis, ta ce wannan shi ne lokacin da ya dace Portugal ta raba gari sa kocin.