✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Pogba ba zai buga Gasar Cin Kofin Duniya ba

Dan wasan na fama da rauni tun bayan barin Manchester United.

Dan wasan tsakiyar Juventus kuma dan kasar Faransa, Paul Pogba ba zai buga Gasar Cin Kofin Duniya ba da za a yi a kasar Qatar, sakamakon rauni da yake fama da shi.

Wakilin dan wasan Rafaela Pimenta ne ya bayyana haka ga manema labarai a yammacin ranar Litinin.

Pogba na fama da ciwo a gwiwarsa, lamarin da ya hana shi tabuka abun a-zo-a-gani tun bayan raba gari da kungiyarsa ta Manchester United.

Dan wasan ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa Faransa ta lashe Gasar Kofin Duniya a shekara hudu da suka wuce.

Pogba ya bar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, watanni shida da suka wuce, sai dai ya gaza taimaka wa kungiyar ta Juventus da ke fama a gasar Seria A, sakamakon rauni da yake fama da shi.

Dan wasan dai ya rattaba wa Juventus hannu kan kwantaragin shekara hudu a karo na biyu.

Mai shekara 29 a duniya, ya buga wa kungiyarsa wasanni biyu ne kacal sakamakon raunin da ya samu, bayan sake dawowarsa kungiyar a karo na biyu.

Wannan ta sa ba zai sami damar wakiltar kasarsa ba a Gasar Cin Kofin Duniyar da za a fara a ranar 20 ga watan Nuwamba, 2022, a kasar Qatar.