✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Pizzar dankalin Turawa

. Dankalin Turawa . Kwai . Jajjagagen attarugu da albasa . Sinadarin dandano . Man gyada . Kori da kayan kanshi .Cikwin Bature (Chease)  …

. Dankalin Turawa

. Kwai

. Jajjagagen attarugu da albasa

. Sinadarin dandano

. Man gyada

. Kori da kayan kanshi

.Cikwin Bature (Chease)

 

Yadda ake yi:

Da farko uwargida za ki dafa dankalin Turawa sai a fere bayansa sannan ki yanka shi kanana ki ajiye shi a gefe.

Sai ki samo kwanonki ki fasa kwai a ciki sai ki  dauko jajjagaggen attarugu da albasa ki zuba a ciki. Ki kuma zuba kayan kanshi da kori da sinadarin dandano da gishiri sai ki jujjuya .

Sannan sai ki dauko yankakke kuma dafaffen dankalinki, ki juye a ciki sai ki juya. Idan ya juyu sai ki dauko farantin gashi (oben), ki shafa mai a jiki sannan ki juye wannan hadin a kai, sannan ki barbada chikun kanti wanda kika gurza a kai (chease) sai ki sa a abin gashi (oben) Idan ya gasu za ki ji yana kanshi.

Amma za ki iya yin wannan Pizzar ta hanyar soyawa. Ma’ana za ki iya yin amfani da kwanon suya sai ki zuba mai a ciki sannan ki juye wannan hadin a ciki.

Sai ki kuma dauko gurzajjen cikwin nan ki barbada a kai sai ki soya. Kowace hanya kika bi (ma’ana gashi ko suya) za ki iya.