An sako dan tseren nan na kasar Afirka ta Kudu Oscar Pistorius daga gidan yari, shekara daya bayan an daure shi sakamakon samunsa da aka yi da laifin kashe buduruwarsa Reeba Steenkamp.
An sako Pistorius ne kwana daya kafin ranar da hukumomi a kasar suka sanar da cewa za a mayar da shi zaman daurin talala na sauran wa’adin da ya rage a daurin shekaru 5 da aka yanke masa.
Hukumomi a kasar sun saki dan tseren ne a wani tsari da za a ci gaba da sa masa ido daga gidansa.
Dama tun a lokacin da aka yanke wa Oscar Pistorius hukuncin, ta bayyana cewa dan tseren zai iya samun irin wannan sassauci a gaba. Sai dai a wanncan lokaci, ba a bayyana wa jama’a sharuddan sassaucin ba, amma da dama sun san ba za a makala na’urar lantarki a jikinsa ba wadda za ta rika samar da bayanai game da shi.
Yanzu za a takaita zirga zirgar sa, sannan ba za a bari ya mallaki bindiga ba, sannan za a rika yi masa gwajin kwakwalwa a kai a kai a gidan Kawunsa inda zai ci gaba da zaman daurin talala. Ana kuma sa rai, za a sa dan tseren ya yi wa jama’a aikin tiki na tsawon wani lokaci.