Kamfanonin sadarwa na Phase3 da YahClick sun kulla kawancen samar da sadarwar intanet mai karfi ga talakawa da yankunan karkara a Arewacin Najeriya.
Hadin gwiwar a cewar Phase3 zai taimaka wajen samar da hanyar sadarwa mai amfani da tauraron dan Adam a fadin Najeriya tare da bada fifiko ga kauyukan da a baya ba su samun layin sadarwa yadda ya kamata.
- Mai gadin kasuwa ya sace wayoyin miliyan N1.5
- Ba a ce za a tsige Buhari ba kuma ba a ce… — Sanata Abdullahi Yahaya
Babban jami’in kamfanin, Muhammed Bashir ya ce, “Shirin zai samar da sadarwa mai rahusa da saukin samu tare da bunkasa zamantakewa da kuma tattalin arziki a kauyuka.”
Bashir ya ce hadakar Phase3 da YahClick zai samar da wadatar intanet mai inganci ga ’yan Najeriya da ma ’yan kasuwa.
Tun a 2006 ne kamfanin Phase3 ya samu lasisin gudanarwa a Najeriya daga Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC).
Ayyukan kamfanin Phase3 za su kai har kasashen ECOWAS, irin su Ghana da Jamhuriyar Benin da Togo da Nijar da Kamaru da Chadi da kuma kasuwannin kasa da kasa.
YahClick kuma ayyukansa za su shafi kauyuka a yankunan Gabas ta Tsakiya da Afirka da Kudu maso Yammacin Asiya da sauransu.