✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Peter Obi ya san bai ci zaben 2023 ba —Wole Soyinka

Magoya bayan Peter Obi sun yi ca a kan Farfesa Wole Soyinka, bayan ya ce Obi da LP sun san ya fadi zaben.

Magoya bayan dan takarar shguaban kasa na Jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi sun yi ca a kan fitaccen marubuci Farfesa Wole Soyinka, bayan da ya ce Peter Obi da kansa ya san ya fadi zaben.

A ranar Laraba ne magoya bayan Obi suka yi wa farfesan dirar mikiya a kafofin sada zumunta bayan da ya maimaita matsayin nasa cewa Obi da jam’iyyar LP sun san bai ci zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu ba.

Wole Soyinka ya fadi haka ne kimanin mako guda bayan Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa na 2023 ta kori karar Obi ta kalubalantar nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben.

Soyinka ya yi furucin nasa ne a taron kwana biyu na masana da masu kirkira domin kawo ci gaba da magance matsalolin a Afirka mai suna ‘Africa in the World’ na 2023, da ke gudana a birnin Stellenbosch na kasar Afirka ta Kudu.

Idan za a iya tunawa a watan Maris bayan hukumar zabe (INEC) ta sanar da Tinubu a matsayin wanda ya ci zaben, mataimakin Peter Obi, Datti Baba-Ahmed, ya bukaci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaurace wa taron mika mulki ga Tinubu.

Jam’iyyar kuma ta lashi takobin kalubalantar nasarar Tinubu har zuwa Kotun Koli.

Borin kunya

Amma da yake jawabi a wurin taron a ranar Laraba, Soyinka ya ce daga Peter Obi har jam’iyyar LP duk sun san ba su suka ci zaben shugaban kasa ba, amma suke “fakewa da karya” wajen tunzura matasa su yi zanga-zanga.

Duk da cewa ya zargi jam’iyyar da mamaye kungiyar kwadago gabanin zaben 2023, amma ya yaba mata bisa yadda ta rage karfin manyan jam’iyyun APC da PDP a siyasar Najeriya.

Ya ce, “Ina fada da babbar murya cewa na uku jam’iyyar Peter Obi ta zo a zaben ba na biyu ba, kuma shugabannin jami’iyyar sun san hakan, amma suke so su yi amfani da karya” don cin-ma burinsu.

“Jam’iyyar ta gina zanga-zangarta a bisa karairayi, ga kuma irin kalaman barazana da dan takarar mataimakin shugaban kasarta yi ga bangaren shari’a da sauransu.

“Wace irin gwamnati za su kafa a haka? Ba su ma san cewa amfani da su aka yi ba. Kafin zabe akwai wasu da suka rika futowa, har da wasu tsoffin janar-janar na soji suna kira da a kafa gwamnatin rikon kwarya, alhali ko zaben ba a yi ba.”

Magoya bayan LP sun yi ca

Wadannan kalaman sun fusata magoya bayan LP, musamman a Twitter, inda daga cikinsu, @aai_austin, ya rubuta cewa, “Karya kake, mai tayar da tarzomar da ya mamaye gidan radio da bakin bindiga mai yada kungiyoyin asiri a jim’o’in Najeriya.”

Malcolm Omirhobo, ya ce, “Soyinka na rudar al’ummar duniya cewa Peter Obi bai ci zabe ba, amma ya ki ce uffan kan shin an yi zaben cikin gaskiya da sahihanci kuma a fili.”
Mikael Bernard, ya ce, “Soyinka na da kabilanci. Ya kawar da kai daga batun takardun karatun Tinubu na bogi, zargin safarar miyagun kwayoyi, duk da nufin kawar da hankalin mutanen Najeriya da karairayinsa.”

@FemiLakers kuma ya ce, “Amma ai [Obi] ya ce zabe a (sic) a Legas da Abuja, wasu farfesoshin ma dai ’yan kwangilar siyasa ne.”

Amma kuma wani mai suna @aliyusalehjnr1, ya goyi bayan Soyinka, da cewa, “Kowa, har shi Obi ya san haka. Amma ban san me suke tunani ba.