✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Pele ya sake angwancewa yana da shekara 75

Tsohon fitaccen dan wasan kwallon kafar nan na duniya dan kasar Brazil, Edson Arantes do Nascimento da aka fi sani da Pele ya angwance yana…

Tsohon fitaccen dan wasan kwallon kafar nan na duniya dan kasar Brazil, Edson Arantes do Nascimento da aka fi sani da Pele ya angwance yana da shekara 75 da amaryarsa wata ’yar kasuwa mai shekara 42 mai suna Marcia Cibele Aoki a wata kwarya-kwaryar hidima da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Tsohon dan wasan ya auri masoyiyar tasa ce ta tsawon shekara shida ne a garin Sao Paulo.
Pele ya shaida wa kafar labarai ta O Estado de Sao Paulo cewa yanzu ya samu soyayya ta hakika kuma ta har abada.
Marcia Cibele Aoki ta kasance tana yi masa rakiya zuwa duk wani taro ko zuwa asibiti don duba lafiyarsa tun shekarar 2012.
Aure biyu da ya yi a baya sun yi shekara 10 ne inda ya haifi ’ya’ya biyar, uku da matansa ta farko sai biyu da matarsa ta biyu.
Pele wanda ake cewa ya fi kowane dan kwallo iya wasa a tarihi ya ci kwallo 1,281 a wasanni 1,363, kuma ya buga wa kasar Brazil sau 91 a tsakanin 1957 zuwa 1971 kuma ya buga wa kungiyar Santos FC da kuma kungiyar New York Cosmos.