Iyalan Pele, tsohon fitaccen dan wasan Brazil da duniya, sun ziyarce shi a asibitin da yake jinya a Sao Paulo, babban birnin kasar, sakamakon ciwon daji, koda da kuma zuciya da yake fama da su, kamar yadda ’yarsa ta sanar a shafinta na sada zumunta.
A ranar Asabar ne dansa Edinho, wanda a baya-bayan aka ba shi aikin horas da kungiyar Londaria da ke buga Gasar Seria B, tare da ’yan uwansa mata, Flavia da kuma Kely Nascimento, suka ziyarci mahaifin nasu.
Kely ta wallafa hoton matar Pele, Marcia Aoki da sauran ’yan uwanta da suka taru a asibitin da Pele ke jinya, duk da cewa ba su wallafa hoton tsohon gwarzon dan kwallon duniyan ba.
A ranar Laraba, asibitin da yake kwance ya sanar cewa Pele da ke fama da ciwon daji na hanji yana samun sauki sosai, sai dai ana ba shi kulawa a kan ciwon koda da zuciya.
Daga bisani ’ya’yansa mata suka sanar cewa zai ci gaba da kasancewa a asibiti, kuma a can zai yi Kirsimeti.
Pele dai ya lashe Gasar Kofin Duniya a 1958 lokacin yana dan shekara 17, inda ya zura kwallaye uku a wasan Kwata-Fainal da kuma karin kwallaye biyu a Wasan Karshe.
Shi ne dan wasa daya tilo a tarihi da ya taba lashe Gasar Kofin Duniya har uku; a shekarar 1958, 1962 da 1970.
A baya-bayan nan Pele ya sha fama da rashin lafiya, har ta kai ga an koma yi masa amfani da na’urar tallafa wa mara lafiya yin numfashi.
An kwantar da shi a asibiti ne a ranar 29 ga watan Nuwamba bayan likitoci sun ce yana bukatar kulawa sosai saboda ciwon daji, bayan tiyatar cire masa kari a hanjinsa a watan Satumban 2021.
Tawagar ’yan wasan Brazil ta nuna goyon bayanta ga gwarzon dan kwallon nata a wasan da ta lallasa Switzerland da ci 4, a matakin ’Yan 16 na Gasar Kofin Duniya da aka kammala a Qatar.