Shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya dan kasar Brazil, Pele, ya rasu yana da shekara 82.
Pele wanda ya rasu ranar Alhamis bayan fama da rashin lafiya shi ne dan wasan kwallon kafa da ba a taba yin irinsa ba.
Ga wasu muhimman abubuwa game da shi.
- Sunansa na asali Edson Arantes do Nascimento, kuma haife shi a shekarar 1940, sannan ya fara lashe Gasar Cin Kofin Duniya tun yana da shekara 17 a duniya.
- Shi ne dan kwallon kafa tilo da ya lashe Gasar Cin Kofin Duniya sau uku — 1958, 1962 da kuma 1970
- Ya shekara 21 yana murza leda kuma yana cikin bakaken fata 20 da suka fi shuhura a duniya a karni na 20.
- Pele mai sanya riga mai lamba 10, ya zura kwallo fiye da 1,280 kuma yi tashe tare da gwarzo dan wasan kwallon kafa na Ajentina, Diego Maradona mai riga mai lamba 10.
- Tun a watan Nuwamba aka kwantar da shi a asibiti, sakamakon cutar kansa, wadda daga baya ta yi sanadiyar daina aikin wasu sassan jikinsa, har ta yi ajalinsa.
- Iya murza ledarsa ya sa ake masa lakabi da Sarkin Kwallon kafa, wadda ake ganin ya kawo wa sauyi da salonsa na taka leda mai kayatarwa da ke kama da rawar Samba ta kasar Brazil.
- Ya lashe gasanni 10 a kulob din Santos sannan a 1977 ya lashe Gasar North American Soccer League a kungiyar New York Cosmos.
- Ya dawo buga kwallo yana da shekara 34, bayan ya yi ritaya, in da ya yi wasa na tsawon kaka uku a kulob din Cosmos na kasar Amurka domin tallata harkar tamola.
- Ya ri ritaya daga buga kwallo a shekarar 1977.
- Ya rasu a ranar Alhamis 29 ga Disamba 2022, kwana 10 baya kammala Gasar Cin Kofin Duniya na 22 kuma na farko a yankin Kasashen Larabawa, wadda Qatar ta dauki nauyi.