✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP za ta tsawaita wa’adin shugabancin Makarfi

A ranar Talatar da ta gabata ne babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kafa wani kwamiti wanda zai shirya babban taron jam’iyyar, inda ake sa…

A ranar Talatar da ta gabata ne babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kafa wani kwamiti wanda zai shirya babban taron jam’iyyar, inda ake sa ran zai duba yadda za a tsawaita wa’adin shugabancin Sanata Ahmed Makarfi, wanda ya yi nasara kan bangaren Sanata Ali Madu Sheriff  a kotun koli.

Kwamitin, wanda Gwamna Ifeanyi Okowa na Jahar Delta da tsohon Gwamnan Jahar Jigawa, Alhaji Sule Lamido za su jagoranta, zai duba yiwuwar kara wa’adin Makarfin ne bisa ga tanajin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Haka zalika jam’iyyar ta bayyana cewa, nasarar da Makarfi ya yi a kotun koli a matsayin sahihin shugabanta, za ta ba shi karfin hada kawunan ‘ya’yan jam’iyyar a fadin kasar nan, domin tunkarar Jam’iyya mai mulki ta APC a zaben 2019 dake tafe.

Kwamitin wanda ya sha alwashin cewa zai bai wa jam’iyya mai mulki ta APC mamakin gaske, kasancewar PDP ta girmi APC sannan kuma ta fi ta ilimin siyasa. Kana kuma ya yi kira ga bangaren da ya sha kaye na Sanata Ali Madu Sherif da su zo a hada karfi da karfe wajen cimma cikakkiyar nasarar da ake bukata don dawo da Najeriya cikin hayyacinta.

Wasu jiga-jigan jam’iyyar sunbayyana cewa wannan mataki da jam’iyyar ta dauka na iya kai ta ga nasara a zabe mai zuwa, bisa nuni da cewa tulin matsalolin dake addabar kasar nan ciki har da rashin ayyukan yi za su iya baiwa jam’iyyar damar amshe mulki daga hannun APC a 2019.