Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP, ta mayar da martani kan furucin da jam’iyyar APC mai mulki a kasar ta yi na cewa ta yi shirin ci gaba da kasancewa a kan karagar mulkin kasar har na tsawon shekara 32.
Shugaban riko na jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Bunin a Jihar Yobe ne ya yi furucin haka a jiya Talata yayin kaddamar da kwamitin tuntuba da tsare-tsare na jam’iyyar a birnin Abuja.
- An yi wa mutum 215,277 rigakafin Coronavirus a Najeriya
- Uwar tagwaye ta yi wa daya zanen tattoo don bambance su
Sai dai PDP ta bakin mai magana da yawunta Mista Kola Ologbondiyan, ta yi masa raddi da cewa jam’iyyar APC ta fara shirya komatsonta don sauka daga kujerar mulkin kasar a shekarar 2023.
A cewar Mista Kola, yanzu haka ’yan Najeriya sun shirya tsaf domin fatattakar jam’iyyar APC a babban zaben kasa mai zuwa don sun gaji da ukubar da suke sha a karkashin jagorancinta.
Kazalika, PDP ta ce ikirarin da jam’iyyar APC ta yi na yi wa mambobinta miliyan 36 rajista a fadin tarayya shaci fadi ne kuma hakan ba zai yi wani tasiri ba a kan ’yan kasar.
“PDP ba ta yi ko gizau ba da ikirarin da Gwamna Mai Mala Buni ya yi, sannan kuma ba ma shakkar karfin da APC ke ganin tana da shi na amfani da Hukumar Zabe da wakilan shari’a da kuma gayyato bata gari da za ta yi daga wasu kasashe domin su taimaka mata wajen dagula al’amura a lokacin zabe mai zuwa.”
“Akwai ganganci da rashin tausayi game da furucin Mai Mala Buni, don yana nufin ’yan Najeriya su nade hannu su ci gaba da zama cikin kunci da talauci da yunwa da rashin tsaro da ukubu na tsawon shekara 32,” a cewar Mista Kola.