Jam’iyyar adawa ta PDP reshen Jihar Kaduna, ta yi Allah-wadai da dage zaben Kananan Hukumomin jihar a karo na uku da Hukumar Zaben Jihar (KADSIECOM) ta yi.
PDP ta bayyana fushinta ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba bayan taron Kwamitin Zartarwanta na jihar.
Sanarwar da Abraham Katoh, Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar ya sanya wa hannu, ta ce ba daidai ba ne hukumar ta tsayar da ranar zaben ba idan ta san cewa ba ta kammala shirin aiwatar da shi.
A cewarsa, “Hukumar ta sake dage zaben zuwa ranar 4 ga Satumban 2021, wanda hakan ya nuna cewa har yanzu ba ta da tabbacin samun kayan aiki kafin lokacin.
A ranar 4 ga watan Yuni KADSIECOM ta shirya gudanar da zaben, amma daga baya ta dage shi zuwa 14 ga Agusta sanna a yanzu ta kuma sake dage shi zuwa 4 ga Satumba, 2021.
PDP ta nuna bacin ranta kan lamarin inda ta bukaci Hukumar Zaben da ta gudanar da aikinta ba tare da tsangwama ko nuna wariya ba.
Aminiya ta ruwaito cewa hukumar ta sanar da sauya zaben a ranar Litinin, inda ta yi nuni da jinkirin isowar wasu kayayyakin da za ta yi amfani da su wajen gudanar da zaben.